“Na Gaji Da Su”: Wani Dan Shekaru 55 Ya Saki Matansa 3 a Rana Daya, Ya Fallasa Zunubansu a Bidiyo
- Wani mutum mai mata da yawa ya zama gauro bayan ya yanke shawarar sallamar dukka matansa guda uku a rana daya
- Mutumin ya magantu kan yadda halayarsu ta sauya bayan ya rasa aikinsa sannan ya ce ya gaji da dukkansu
- Mutumin mai shekaru 55 da yara bakwai ya bayyana aiki mai ban sha'awa da yake yi a yanzu na kula da yaran sauran mutane
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wani mutumin kasar Uganda, Mutiatya, ya saki matansa uku a rana daya, inda suka tafi suka barsa da yara bakwai.
Afrimax ta yi hira da mutumin mai shekaru 55, wanda ya ziyarci kasashe 14, sannan ta bayyana dalilin da yasa ya rabu da matansa.
Mutiatya ya gaji da halayen tsoffin matansa
Mutiatya ya ce ya saki matansa saboda munanan halayensu. Ya tuna yadda abubuwa ke tafiya daidai a bayan har zuwa lokacin da ya rasa aikinsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce gaba dayansu sun sauya sannan suka fara raina shi sannan abun ya kai har sun fara ci masa amana. Ya ce:
"Dalilin da yasa na fatattake su ya kasance saboda munanan dabi'unsu. Da farko, sun kasance masu kirki kuma hazikan mata wadanda suka shirya gina babban gida mai nagarta.
"Daga karshe, sai gaba daya suka fara rashin da'a, abun da ba zan taba iya jurewa ba kuma shawarar da na yanke shine korarsu. Ya kasance mai tsauri amma wanda ya dace domin basa son ci gaba da zama mata masu da'a a gidan."
Mutiatya ya bayyana sabon aikin da ya samu
Uban yara bakwan ya ce yanzu yana kula da yaran sauran mutane. Ya ce yanzu yaransa sun girma kuma suna zaune a kasashe daban-daban.
Domin dogaro da kansa, mutumin, wanda bai da niyan sake aure a gaba, yana siyar da kayan ado na mata da sauran abubuwan da hannunsa ya kai kansu.
Abun da Mutiatya ke yi ya dauka ya ja hankalin mutane
@nelisandikimoscato2497 ya ce:
"Ina fatan ba wai yana amfani da sunan Allah don aiwatar da mugun nufinsa bane."
@nondochirau9664:
"Yaran nan ba za su tsira ba a tare da shi. Abubuwa da dama na faruwa a duniyar nan ban yarda da shi ba."
Mutumin da ya kirkiri tutar Najeriya ya rasu
A wani labari na daban, mun ji cewa Allah ya yi wa mutumin da ya kirkiri tutar Najeriya, Pa Michael Taiwo Akinkunmi (OFR), rasuwa.
Pa. Akinkunmi, mai shekaru 84 ya mutu a safiyar ranar Talata, 29 ga watan Agusta, bayan yar gajeruwar rashin lafiya.
Asali: Legit.ng