Saki: Mata ta mayarwa miji sadakin N28,000 da ya biya yayin aurenta shekaru 7 da suka shude
- Wata mata a Abuja ta mayarwa mijinta N28,000 na kudin sadakin da ya biya lokacin da ya aure ta
- Hakan ya biyo bayan matar da kai shi kotu inda ta nemi a raba aurensu domin bata ra'ayin cigaba da zama da shi
- Mijin ya nemi kotu ta basu dama su yi sulhu amma hakan bai yi wu ba don haka ya ce ta biya shi kafin ya sake ta
An mayar wa wani mutum mai suna Boyi Adamu sadakinsa N28,000 bayan wata kotu mai daraja ta 1 da ke zamanta a Gwagwalada Abuja ta raba aurensa sakamakon korar da matarsa, Hauwa Abdulkarim ta shigar a kotu.
Hauwa, wace ke zaune a Anguwar Dodo a Gwagwalada, a cikin karar da ta shigar da ta bata ra'ayin cigaba da zama da mijinta bayan shekaru bakwai da aurensu, Daily Trust ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Hotunan hatsabibin mai garkuwa da aka kama yayin da ya tafi karbar kuɗin fansa
Adamu, wanda ke zaune a Rafin-Zurfi, da farko ya nemi kotu ta bashi daman yin sulhu da matarsa amma hakan bai yiwuwa ba inda matar da dage sai ya sake ta.
Don haka, ya nemi matar da mayar masa da jimillar kudi N203,500 daga matarsa a matsayin kudin da ya kashe wurin aurenta.
Sai dai daga bisani, ma'auratan biyu sun cimma matsaya a kan N28,000 wanda shine sadakin da ya biya lokacin da zai aure ta.
DUBA WANNAN: Buhari ya naɗa ni shugaban soji ne saboda ƙaunar da mahaifina ke masa, in ji Buratai
Alkalin, Adamu Isah, ya raba auren bayan da matar da mayarwa mijinta kudin sadakinta N28,000 da ya biya.
A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.
Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng