Gwamnan Neja Umaru Bago Ya Ce Suna Tattaunawa Da 'Yan Bindiga Domin Su Ajiye Makamai

Gwamnan Neja Umaru Bago Ya Ce Suna Tattaunawa Da 'Yan Bindiga Domin Su Ajiye Makamai

  • A ƙoƙarin ganin an samu zaman lafiya, gwamnatin jihar Neja na kan tattaunawa da 'yan bindiga
  • Gwamnan jihar Umaru Mohammed Bago ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai
  • Ya ce gwamnatin za ta iya yi wa 'yan bindigar afuwa idan suka amince suka ajiye makamansu

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago ya ce a shirye gwamnatinsa take ta yi wa 'yan bindigar jihar afuwa muddun za su yi abinda ake so.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata, bayan wata ziyara da ya kai ofishin Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris a Abuja.

Umaru Bago ya ce suna kan tattaunawa da 'yan bindiga
Gwamnan Neja Umaru Bago ya ce suna kan tattaunawa da 'yan bindiga domin su ajiye makamai. Hoto: Umaru Mohammed Bago
Asali: Facebook

Dalilin tattaunawar gwamnan da 'yan bindiga

Gwamna Bago ya ce za su yi wa 'yan bindigar afuwa ne idan za su ajiye makamansu domin a samu zaman lafiya a jihar Neja da kewayenta kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Zai Biya Mazauna Abuja Diyyar N825m,.Ya Bayyana Dalili

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan ya ce yanzu haka suna kan tattaunawa da 'yan ta'addan jihar, kuma ƙofar yi mu su afuwa a buɗe take muddun za su ajiye makaman na su.

Sai dai gwamnan ya ce a shirye gwamnatin jihar take ta yaƙi ɓarayin idan suka ƙi amincewa da batun tattaunawar da aka zo mu su da ita.

Shugaba Tinubu na ƙoƙarin shawo kan matsalar tsaro

Da yake magana kan matsalar tsaron da ta addabi sauran sassa daban-daban na ƙasar nan, gwamnan ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba komai zai daidaita.

Ya ce akwai abubuwan da jami'an tsaro suke yi ta ƙarƙashin ƙasa, wanda bai dace a zo ana bayyanawa al'umma su ba kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Ya kuma ba da tabbacin cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu na iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin an kawo ƙarshen matsalar tsaron da ta dabaibaye ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Soja 36: Babban Hafsan Tsaro Ya Fadi Abinda Za Su Yi Wa 'Yan Ta'addan Da Suka Halaka Sojoji a Neja

'Yan bindiga sun fara tserewa daga dazuzzukan jihar Neja

Legit.ng a baya ta yi rahoto da ke nuni da cewa 'yan bindigan da suka addabi jihar Neja sun soma arcewa daga dazuzzukan jihar.

Hakan dai ya biyo bayan farmakin da sojoji ke kai mu su babu ƙaƙƙautawa tun bayan ta'adin da suka yi mu su a kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng