Jami'ar Chicago Ta Kulle Manhajar 'Twitter' Bayan 'Yan Najeriya Sun Dame Su Da Sakwanni Kan Takardun Tinubu

Jami'ar Chicago Ta Kulle Manhajar 'Twitter' Bayan 'Yan Najeriya Sun Dame Su Da Sakwanni Kan Takardun Tinubu

  • Al'amura na kara rikirkicewa yayin da 'yan Najeriya su ka bukaci jami'ar Chicago da ke Amurka ta sa ke takardun karatun Shugaba Tinubu
  • Jami'ar a karshe ta rufe manhajarta na 'Twitter' yayin da 'yan Najeriya ke bulbula mata sakwanni don ta sake takardun karatun Tinubu
  • Tinubu ya bayyana cewa ya kammala karatun digiri dinsa a jami'ar inda ake kokwanton sahihancin takardun nasa

Chicago, Amurka - Jami'ar jihar Chicago da ke Amurka ta kulle manhajarta na Twitter mai suna @ChicagoState kan yawan sakwanni na 'yan Najeriya kan takardun Shugaba Tinubu.

Jami'ar ta Amurka ta saka wani mataki a manhajar tata don kada kowa yaga abin da ke manhajar ta idan baka bibiyarta, kamar yadda Legit.ng ta tattaro.

Jami'ar Chicago sun rufe manhajarta ta 'Twitter'
Jami'ar Chicago Ta Dauki Mataki Kan 'Yan Najeriya Da Ke Damunsu Da Sakwanni. Hoto: @OfficialABAT/@ChicagoState.
Asali: Twitter

Meye ya tilasta jami'ar Chicago rufe 'Twitter' kan Tinubu?

Kara karanta wannan

"Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Shiga Ruɗani" Atiku Ya Ƙara Bankaɗo Abinda Tinubu Ya Yi a 1999 da 2023

Wannan na zuwa ne bayan 'yan Najeriya da dama sun caccaki jami'ar don ta ki sake takardun karatun shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan kasar sun damu jami'ar ta bayyanawa duniya takardun karatun nashi ganin yadda ake shari'ar zabe da bai kammala ba.

Takardun Tinubu sun nuna cewa ya karanta harkar Gudanar da Kasuwanci da Lissafin Kudade a shekarar 1979, cewar The Whistler Nigeria.

Meye Atiku ke nema a jami'ar Chicago Kan Tinubu?

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar na daga cikin wadanda su ke cikin shari'a da Shugaba Tinubu kan zaben da ya gabata.

A baya jami'ar ta yanke hukuncin sake takardun karatun Shugaba Tinubu yayin da 'yan kasar ke dakon jira.

Jam'iyyar PDP a cikin wata sanarwa ta bayyana a shafinta na Twitter a ranar 24 ga watan Agusta cewa jami'ar ta saki takardun ga kotu inda tun a farko ta nemi bukatar hakan.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Kwastomomi Sun Rage Zuwa Gida Karuwai a Kano, Gidan Magajiya Ya Dauki Zafi

Atiku Ya Bukaci Jami'ar Chicago Ta Saki Takardun Tinubu

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bukaci jami'ar Chicago da ta saki takardun karatun Tinubu.

Atiku ya bukaci takardun ne bayan samun sabani a shekarun Tinubu wanda a yanzu haka su ke kotun sauraran kararrakin zabe.

'Yan Najeriya da dama na neman sanin hakikanin gaskiya game da bambanci shekaru da aka samu na shugaban kasa, Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.