Bidiyo: Wata Budurwa Ta Amarce da Dan Kasar Wajen Bayan Ta Kamu a Soshiyal Midiya

Bidiyo: Wata Budurwa Ta Amarce da Dan Kasar Wajen Bayan Ta Kamu a Soshiyal Midiya

  • Wata budurwa 'yar Najeriya ta amarce da rabin rayuwarta, wani bature da suka haɗu a Facebook tun ranar 21 ga watan Yuni, 2020
  • Amaryar ta bayyana cewa ita da masoyinta sun shafe watanni da dama suna soyayya daga nesa kafin daga bisani suka haɗu kuma suka yi aure
  • Masu amfani da shafin TikTok da dama sun taya sabuwar amaryar murna, yayin da wasu mata suka ce suna ta jiran nasu abokin rayuwar

Wata zankadediyar budurwa 'yar Najeriya ta bayyana cewa ta haɗu a abokin rayuwarta watau mijinta a shafin sada zumuntar Facebook ranar 21 ga watan Yuni, 2020.

Matar mai suna, Vicky Crown, ta bayyana yadda ta samu damar haɗuwa da mijin ta yanar gizo da kuma yadda suka fara ƙaunar juna har suka fara soyayya gadan-gadan.

Kara karanta wannan

Wata Mata Ta Haifi Yara 9 Cikin Shekaru 13, Ta Ce Saura Na Nan Tafe

Haduwar Facebook.
Bidiyo: Wata Budurwa Ta Amarce da Dan Kasar Wajen Bayan Ta Kamu a Soshiyal Midiya Hoto: @Vickycrown
Asali: TikTok

Bayan tsawon shekara ɗaya suna shan romon ƙauna daga nesa, daga bisani masoyan biyu sun haɗu da juna ido da ido, inda suka rungume juna cikin farin ciki.

Yar Najeriya ta auri farin mutumin da suka haɗu a soshiyal midiya

Ta wallafa wani bidiyo wanda ya nuna ranar da suka ga juna ido da ido bayan shafe watanni da yawa suna kiran bidiyo da aika saƙonnin soyayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Vicky ta bayyana cewa:

"Na haɗu da shi a Facebook ranar 21 ga watan Yuni, 2020 kuma tun daga wannan lokaci zuwa yau, shi ne abu mafi kyau da ya faru da ni a rayuwata."

A halin yanzu dai sun shiga daga ciki watau sun yi aure kuma suna rayuwa cikin farin ciki da jin daɗi bayan shekaru uku da haɗuwarsu a soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Sake Kai Farmaki a Zariya, Sun Yi Awon Gaba Da Bayin Allah

Martanin mutane a TikTok

@MoiAdorable ta ce:

"Na miki murna 'yan mata, nima a Faceook na haɗu da rabin raina kuma yanzu haka mun yi aure muna farin ciki."

@Busola ta ce:

"Ni bansan kowa ba a Facebook, watakila a Wahtsapp zan haɗu da nawa abokin rayuwan."

@Ma'am Tee ta ce:

"Wai dan Allah taya kuke haɗuwa da masoya ne? Ki taimaka mun yar uwa."

@TITILAYO MI ta ce:

"Ina buƙatar na goge manhajar Facebook kuma na ɗauko sabo ko Allah zai sa nawa mijin ya gano inda nake."

Wata Mata Ta Haifi Yara 9 Cikin Shekaru 13, Ta Ce Saura Na Nan Tafe

A wani labarin kuma Wata yar kasar China mai suna Tian Dongxia da mijinta Zhao Wanlong sun ja hankalin jama'a bayan sun haifi yara tara a cikin shekaru 13.

Da aka tambayeta kan dalilin da yasa take haihuwa ba kakkautawa, ta bayyana cewa bata so ta "yi asarar kwayoyin halittar mijinta."

Kara karanta wannan

"Zaman Jira Ya Kare": Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Wuff Da Wani Bature, Bidiyon Aurensu Ya Dauki Hankula

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262