Tsohon Shugaban Hukumar NBS Ya Soki Tsarin Da Aka Bi Wurin Fitar Da Alkaluman Rashin Aikin Yi A Najeriya
- Tsohon shugaban hukumar NBS, Yemi Kale ya soki tsarin yadda hukumar ta yi amfani da shi wurin bayyana rashin aikin yi
- Kale ya ce tsarin da hukumar NBS ta yi amfani da shi ya sabawa yadda hukumomin kasa da kasa ke amfani da shi
- Ya ce yin amfani da sa'o'i a wurin gwada rashin aikin yi a kasa ba zai ba da ma'ana ba musamman a wannan lokaci
FCT, Abuja - Tsohon shugaban Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), Yemi Kale ya kalubalanci yadda aka samo bayanai na rashin aikin yi a Najeriya.
Ya ce a lokacinsa ya ki amincewa da a sauya akalan yadda ake samo bayanai saboda bai gamsu da su ba, Legit.ng ta tattaro.
Meye Kale ya ce kan alkaluman NBS?
Kale ya bayyana haka ne bayan hukumar ta fitar da alkaluma cewa an samu raguwar rashin aikin yi da kaso 4.1.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Alkaluman su ka ce a lokacin da Kale ke shugabantar hukumar a farkon zango na 2021 rashin aikin yi ya kai kashi 33.
Kale ya ce yadda su ka yi amfani da sa'o'i wurin gwajin bai ba da ma'ana ba.
Inda ya ce yawan kudin da mutum zai samu idan ya yi sa'o'i 20 ya na aiki a Najeriya bai wuce sa'a daya ba a Amurka.
Wane martani NBS ta yi kan Kale?
A martaninshi, daraktan yada labarai na hukumar, Wakili Ibrahim ya ce ba a taba lalataccen shugaban hukumar irin Kale ba.
Ya ce a lokacin Kale hatta wutar lantarki ba ya aiki a ofishinsa inda ya ce makudan kudade sun bace a lokacinsa.
Ya zargi Kale da kin barin ofis kusan shekaru 10 har sai da aka tsige shi da karfi, kamar yadda Business Hallmark ta tattaro.
Rashin Aikin Yi Ya Ragu Sosai A Najeriya, NBS
A wani labarin, Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS ta bayyana cewa rashin aikin yi ya ragu da kashi 4.1 a farkon wannan shekara da muke ciki.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar ta tabbatar da cewa a karshen shekarar 2022, alkaluman sun kai kashi 5.3 na rashin aikin yi.
Asali: Legit.ng