Gwamna Inuwa Yahaya Ya Ba Da Umurnin Rufe Gidajen Gala Da Ke Gombe
- Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya ba da umarnin kafatanin gidajen gala da ke jihar
- Matakin ya biyo bayan korafe-korafen da jama'a ke yi kan miyagun laifukan da ake aikatawa
- Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ba da umarnin rufe kafatanin gidajen gala da ke jihar Gombe ba tare da ɓata lokaci ba.
Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Dalilin Inuwa na rufe gidajen gala na Gombe
Sanarwar ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan korafe-korafen da jama'a suka shigar kan abubuwa na rashin ɗa'a da kuma aikata miyagun laifuka da ake yi a gidajen galan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ƙara da cewa gwamnan ya bai wa jami'an tsaron jihar umarnin tura mutanensu waɗannan wurare domin tabbatar da cewa an dauki mataki kan lamarin kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.
Ya umarci jami'an rundunar 'yan sanda, jami'an tsaro na fararen hula (NSCDC), da kuma jami'an 'Operation Hattara' da su tura mutanensu wuraren da abin ya shafa domin tabbatar da an bi umarnin.
Gidajen galan da gwamna Yahaya ya ba da umarnin a rufe
Gidajen galan da wannan umarni ya shafa sun haɗa da: Jami’a Gidan Wanka na Mile 3 kan titin Yola, White House Theatre (Babban Gida) na titin Yola, Gidan Lokaci, da kuma Farin Gida Entertainment II duk a cikin garin Gombe.
Karin gidajen su ne: Gidan Zamani Entertainment, Albarka Entertainment, gidajen gala da ke a garin Kuri, Lubo da kuma Kurba da ke a ƙaramar hukumar Yamaltu Deba ta jihar.
Sannan kuma akwai Tauraren Wash da yake a Trailer Park kan titin Bauchi, da kuma gidajen gala da suke a garin Bajoga, ƙaramar hukumar Funakaye kamar yadda sanarwar da ta fito daga gidan gwamnatin ta bayyana.
Inuwa ya ce biliyan 2 kawai jiharsa ta samu na tallafin Tinubu
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan ƙorafin da gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi kan kuɗaɗen tallafi har naira biliyan biyar da Tinubu ya aikawa kowace jiha.
Inuwa ya ce naira biliyan biyu ce ta iso asusun jiharsa, inda ya shawarci al'ummar jihar su mayar da hankalinsu a kan noma.
Asali: Legit.ng