Tinubu Ya Roki Ministoci Da Su Fada Masa Gaskiya Idan Ya Kauce Hanya
- Shugaban kasa, Bola Tinubu ya jagoranci ganawar majalisar zartaswa ta ministoci na farko tun hawanshi karagar mulki
- Tinubu ya roki ministocin da kada wani ya ji tsoron fada masa gaskiya idan ya yi kuskure inda ya ce Allah ne kadai ba ya kuskure
- Tun farko a jawabinsa, Shugaba Tinubu ya taya sabbin ministocin murna inda ya gargade su da kada su manta da al'umma da suka zabi gwamnatinsa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci ganawar farko na majalisar zartaswa da ministoci a fadarsa da ke Abuja.
Tinubu yayin jawabinsa, ya taya sabbin ministocin murna inda ya bukace su da su sani sun zo yi wa jama'a aiki ne, PM News ta tattaro.
Wane jawabi Tinubu ya yi ga ministoci?
Shugaban ya bayyanawa ministocin cewa shi dan Adam , duk wanda ya ga kuskure kada ya ji tsoron fada masa inda ya kara da cewa Allah ne kadai ba ya kuskure.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce ya na kallon kansa a matsayin direba yayin da ko wane minista daga cikinsu zai zamo karen mota, Legit.ng ta tattaro.
A cewarsa:
"Ya kamata mu tabbatar da kasar nan ta ci gaba, na karbi wannan ragamar tare da nada ku don yi wa kasa aiki.
"Akwai abubuwa da dama da ake ganin ba su da sauki, amma a wurinku komai mai yiyuwa ne.
"A shirye na ke don karbar gyara, Allah ne kadai ba ya kuskure, idan na kauce hanya kada ku ji tsoron taro ni."
Wane roki Tinubu ya mika ga ministocin?
Shugaba Tinubu ya kara da cewa akwai matsalar rashin aikin yi a kasar, ya bukace su da su kawo sauyi musamman wurin zuba hannun jari a kasar.
Tinubu ya ce idan akwai rashin tsaro babu yadda masu zuba jari za su zauna a kasa.
Ya ce lokaci ya yi da ya kamata a shawo kan masu zuba hannun jari zuwa kasar kamar yadda ko wane shugaba ke kokarin yin haka.
Daga cikin kusoshin gwamnati da su ka halarci taron akwai mataimakinsa, Kashim Shettima da shugaban ma'aikata, Femi Gbajabiamila.
Sauran sun hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da kuma jagorar ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Folashade Yemi-Esan.
Tinubu Ya Nada Sabbin Ministoci
A wani labarin, shugaba Tinubu ya nada sabbin ministoci bayan gama tantance su a majalisar Dattawa.
Wannan na zuwa ne bayan ta tantance ministoci 45 cikin 48 inda uku daga ciki su ke jiran bincike na musamman.
Asali: Legit.ng