Shehu Sani Ya Jeri Fitattun ’Yan Najeriya da Ya Kamata Shugaban Kasa Tinubu Ya Nada Ministoci

Shehu Sani Ya Jeri Fitattun ’Yan Najeriya da Ya Kamata Shugaban Kasa Tinubu Ya Nada Ministoci

  • Sanata Shehu Sani ya kawo wasu fitattun ‘yan Najeriya da ya ke ganin ya kamata shugaba Tinubu ya yi la’akari da su a matsayin ministoci
  • Tsohon sanatan ya ba da shawarar cewa mutane irin su Jay Jay Okocha, Segun Odegbami, Daniel Amokachi, da Mary Onyali, duk sun dace da mukamin ministocin wasanni
  • Sani ya kuma ambaci Allen Onyema, mai kamfanin Air Peace, a matsayin wanda ya fi dacewa da mukamin ministan sufurin jiragen sama

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna – Sanata Shehu Sani, tsohon dan majalisar tarayya daga jihar Kaduna, ya bayyana sunayen wasu fitattun ‘yan Najeriya da ya kamata shugaba Tinubu ya nada ministoci.

Sani, wanda jigo ne a jam’iyyar PDP ya ambaci sunayen ne a wata hira da jaridar Punch ta buga a ranar Lahadi, 27 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Ibrahim Geidam: Muhimman abubuwa 6 da baku sani ba game da ministan harkokin 'yan sanda

Da aka tambaye shi ko wace shawara zai bai wa shugaban kasa idan ya gana da shi, Sani ya ce zai cewa Tinubu ya nada mutanen bisa ga kwazo da kwarewarsu da iya aiki.

Shawarin Shehu Sani ga Tinubu
Shehu Sani ya yi bayanai kan ministocin Tinubu | Hoto: Senator Shehu Sani, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sani, wanda kuma dan rajin kare hakkin bil'adama ne ya ce da zai hadu da Tinubu zai shawarci shugaban kasar da ya nada ministan wasanni daga cikin tsoffin 'yan wasa ko kuma wasu mata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

"Na so in ga ministan wasanni irin su Jay Jay Okocha, Segun Odegbami, Daniel Amokachi, ko Mary Onyiali, ko kuma mutanen da suka sanya rigar wasannin kasarmu."

A kwanakin baya ne dai shugaba Tinubu ya kaddamar da majalisar ministocinsa, inda ya nada Sanata John Enoh a matsayin ministan wasanni.

Allen Onyema a ma'aikatar sufurin jiragen sama

Da yake karin haske, Sani ya ce mai kamfanin Air Peace, Allen Onyema ne ya fi zama wanda zai taka rawar gani a kujerar ministan sufurin jiragen sama.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Kwanaki kadan da yin ritaya, tsohon kakakin soja ya kwanta dama

Jigon na PDP ya shaidawa Punch cewa:

"Na so ministan sufurin jiragen saman da ya kware a fannin sufurin jiragen sama, wani dai kamar Allen Onyema, mai kamfanin Air Peace, da sauran wadanda suka san matsalar sufurin jiragen sama da yadda za su magance matsalar."
"Na so ganin ministan ayyuka a matsayin injiniya, kwararren mutum wanda ya san abin da ake nufi da aikin manyan ayyukan gini, masanin zane-zanen ginin da ya san abin da ake ginawa. Irin mutanen da nake son gani kenan.
"Amma ya iya yin hakan a fannin kiwon lafiya ta hanyar nada (Farfesa Muhammad) Pate, kwararre a fannin likitanci da aka sani a duniya. Ministan Harkokin Waje ya kasance jakadan Najeriya a kasar Jamus, irin wadannan mutane ne masu nagarta."

Shawarin Shehu Sani ga Wike

A wani labarin, tsohon dan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani ya bayyana bukatar ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Ana tsaka mai wuya: Abin da Tinubu ya fadawa Malaman addini kafin su tafi Nijar

A wata hira da jaridar Punch, Sani ya bukaci tsohon gwamnan jihar Ribas, Wike, da ya koma jam’iyyar APC mai mulki saboda ya samu damar yiwa jam’iyyar mai mulki hidima.

Hakazalika, ya ce barinsa PDP zai ba jam’iyyar damar tsayawa kekam a matsayin jam'iyyar adawa mai karfi a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.