“Ki Bar Nan Cikin Kwanaki 8 Ko Kuma” Malaman Ilorin Sun Yi Sabon Barazana Ga Yar Addinin Gargajiya a Bidiyo
- Malaman Musulunci a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, sun yi barazanar yin maganin wata yar addinin gargajiya
- A wani bidiyo da ya yadu, Malaman karkashin jagorancin wani Sola Ayodeji, sun sha alwashin tayar da rigima a garin idan matashiyar ta ki barin harabar cikin kwanaki takwas
- Daya daga cikin malaman ya kuma yi barazanar lalata gaba daya kayayyakin da ke shagon matashiyar, bayan bukatar da suka gabatar kan addinin gargajiya a jihar Kwara
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Ilorin, jihar Kwara - Wasu Malaman addinin Musulunci sun yi sabon barazana ga wata yar addinin gargajiya wato Isese a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
Jaridar Punch ta wallafa wani bidiyo a manhajar X, (wacce aka fi sani da Twitter a baya) da ke nuna yadda malaman Musuluncin suka mamaye shagon yar gargajiyar a Ilorin, don yi mata barazana da ci mata mutunci.
Malaman, karkashin jagorancin wani Sala Ayodeji, sun yi barazanar ta da zaune tsaye idan matashiyar bata tattara ta bar harabar wajen ba cikin kwanaki takwas.
Malaman wadanda yawansu ya kai 15 sun koro bukatunsu, inda daya daga cikinsu ya yi barazanar lalata komai na shagon idan matashiyar bata yi shiru ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yayin da yake magana a harshen Yarbanci, Ayodeji ya ce:
"Cikin kwanaki bakwai, dangin Alaran sun mayar masu da kudinsu sannan su kore su.
"Idan muka dawo cikin kwanaki bakwai sannan muka gan su a nan, lamarin zai munana fiye da wannan.
"Kwamishinan yan sandan na sane da ziyararmu, kun san cewa wannan ba shine karonmu na farko ba, mun san yadda ake abun nan, don haka ku bar garinmu."
Jama'a sun yi martani yayin da malamai suka yi wa yar gargajiya barazana
Juyin Mulki: "Ku Tsaya Cikin Shiri", Sojojin Nijar Sun Tura Muhimmin Sako Ga Dakarunsu Yayin Da ECOWAS Ke Shirin Afka Musu
Yan Najeriya sun garzaya sashin sharhi a X don yin martani kan ci gaban.
@IBROKAMMY ya yi martani:
"Maganar haka take. Gaskiyar batu. Babu barazana a cikin wannan tattaunawar. Ku koma garinku ko kauye ku yi duk abun da kuke so ba a Ilorin ba."
@Kolaqhazim ya ce:
"Wdannan mutanen yan Ilorin ne, haka nima menene matsalar ku kuma kun ce kuna da ilimi, ku bar mutane su yi duk abun da suke so, duniya ce."
@Hay_zedd01 ya ce:
"Yanzu naga dalilin da yasa ake kiran mutanen Ilorin aboki saboda banbancin kadan ne ko babu banbanci tsakaninsu da yan arewa."
Dan Najeriya ya saka siket a wajen daurin aurensa
A wani labari na daban, mun ji cewa wani dan Najeriya ya auri sahibarsa baturiya kuma ya hakan cikin siga da ba za a taba mantawa ba.
A cikin wani bidiyon TikTok da ma'auratan suka wallafa a shafinsu, @majiq.pia, an gano su sanye da kaya da ba a saba gani ba zuwa wajen aurensu.
Asali: Legit.ng