Muna matuƙar buƙatar mazajen aure, ƴan matan Gombe sun koka

Muna matuƙar buƙatar mazajen aure, ƴan matan Gombe sun koka

- Wasu yan mata a jihar Gombe sun koka kan cewa ba su samu mazajen aure ba

- A bisa ga rahoto, Gombe na daya daga cikin jihohin arewa maso gabas da ke da yawan mata marasa aure

- Matan da abin ya shafa sun ce yawancin mazan jihar ba su shirya yin aure ba

A wani lamari mai kama da wasan kwaikwayo, wasu mata marasa aure a jihar Gombe sun yi kukan neman taimako kan rashin samun mazajen aure.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa mummunan lamarin ya ci gaba tsawon wasu shekaru a yankin arewa maso yammacin kasar, inda ta kara da cewa daruruwan mata marasa aure karkashin jagorancin Suwaiba Isa sun mamaye jihar Zamfara.

Sun yi hakan ne don zanga-zangar rashin samun mazajen aure ga kimanin su 8,000 a watan Satumban 2018.

Muna matuƙar buƙatar mazajen aure, ƴan matan Gombe sun koka
Muna matuƙar buƙatar mazajen aure, ƴan matan Gombe sun koka Hoto: @GovernorInuwa
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun sace babban basarake a Ribas, har yanzu ba a san inda yake ba

Legit.ng ta tattaro cewa sarkin Yarbawa a Gombe, Abdulrahim Alao Yusuf, ya ce kashi 60% na mutanen da ba ‘yan asalin jihar bane sun fito ne daga yankin kudu maso yammacin kasar.

Daya daga cikin mazauna jihar Gombe, Godiya Adamu, ta ce shekarunta 35, har yanzu ba ta samu miji ba, tana mai dora alhakin halin da ake ciki kan rashin samun namijin da ke son aure da gaske.

Ta bayyana cewa ta yi soyayya na kimanin shekaru biyar ba tare da sakamako mai ma'ana ba kafin daga baya ta hakura.

Ta ce: “Me zan yi? Ba zan iya cusa kaina ga maza ba idan ba su zo ba. A iya sani na, rayuwa na ci gaba da miji ko babu miji."

Da take magana kan batun, Abigail, mai yara biyu, ta ce da gangan ta zabi ta zama uwa ba tare da aure ba domin ta samu kwanciyar hankali, ta kara da cewa ta zabi zama mara aure ne saboda ba za ta iya zama ta biyu ba a gidan aure.

Ta ce: “Ina zaune a gidana a cikin garin Gombe tare da’ ya’yana. Nice mahaifiyarsu kuma ubansu. Ina da abokai waɗanda suka gwammace kada namiji ya sanar da kasancewar su ga matar gida kuma suna jin daɗin hakan.

“Abin da nake so in ce shi ne mutum ya tafi duk abin da zai sa shi farin ciki. Babu wani sabon abu a rayuwar nan.”

Wata Bafulatana, mai suna Amina, ta ce matsalarta ita ce ta yi karatu, tana mai cewa ta gano cewa yawancin maza a arewa ba sa son auren mata masu ilimi.

Amina ta lura:

“Wataƙila saboda suna ganin ba abu mai sauƙi ba ne a gare su su juya irin wannan matar son ransu. Don haka a wurina, zaɓin shi ne na ci gaba da zama ba aure sannan na zamo uwa da uba ga yarana.”

A cewar rahoton, Rev. Adamu Dauda na cocin ECWA Gospel Church Gombe ya ce lokacin da ya lura cewa lamarin na neman zama mai tayar da hankali, sai ya kira taro da dukkan matasa da ke cocin.

Ya ce: “Ina jagorantar wata kungiya mai mambobi sama da 1,500 daga ciki muna da matasa sama da 800. A yayin taron, mun gano cewa a cikin matasa 800, 487 ba su yi aure ba, don haka na fara daukar matakan magana da su daya bayan daya.

“Abin mamakin shine wasu matan sun gaya min cewa babu wanda ya nemi aurensu. Sannan na tambaya, ba ku ga kowa da kuke so? Wasu sun ce eh, amma ba za su iya zuwa wurin mutumin ba saboda ya saba wa al'adun Afirka. Wannan shi ne fannin da muke dubawa yanzu."

A nasa jawabin, Babban Limamin Masallacin gidan Gwamnati a Gombe, Sheik Dr. Zakariya Hajiya, ya dora alhakin rashin samun mazajen da mata bas a yi a jihar kan talauci.

KU KARANTA KUMA: Ba dan ta'adda bane: FKK ya ambaci gwamnan arewa da ya taimaki Jonathan ya zama shugaban kasa bayan 'Yar'adua

Ya bayyana cewa makudan kudaden da ake kashewa yayin aure wajan yiwa amarya, dangin ta, masallatai da coci-coci sun zama wani nauyi a kansu.

Shehin malamin ya lura da cewa mummunan yanayin da tattalin arziki ke ciki da cutar ta COVID-19 ta haifar da kuma kalubalen tsaro a yankin na arewa maso gabas ya kara dagula lamarin.

Ya ce: “Kudin da aka kashe kan wadannan abubuwa kamar sadaki, kayan sawa, kayan kwalliya, kayan kicin, gado, talabijin, firiji da sauran kayan aikin gida, wanda miji zai samarwa da amarya, dangin ta da sauransu babbar nauyi ne a gare shi."

A wani labarin, Beatrice Williams Auta, ‘yar fim din Kannywood da ta taka rawa a matsayin Stella a cikin shirin Arewa24 'Dadin Kowa’, ita ce mai jin daɗin hira kowane rana.

A tattaunawa da Aminiya, jarumar ta bayyana abubuwa masu ban sha'awa game da kanta.

Ta yi magana kan girma, makarantun da ta yi karatu, rayuwarta ta sirri da kuma abubuwan da za ta sauya a masana'antar finafinan Hausa idan tana da iko.

Ta kuma mayar da martani game da zargin da ake yi cewa akwai 'yan luwadi da madigo a Kannywood sannan ta bayyana wasu kalubalen da ta ke fuskanta a masana'antar. Ji dadin hirar.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel