'Yan N-Power Sun Roki Tinubu Ya Kawo Musu Dauki Kan Rashin Biyansu Alawus Na Watanni 8
- Matasan da ke cin gajiyar shirin N-Power sun koka wa shugaban kasa, Bola Tinubu kan rashin biyansu alawus har watanni takwas
- Sakataren yada labarai na masu cin gajiyar, Gbadebo Adesiyan shi ya yi wannan korafi inda ya ce su na cikin mawuyacin hali
- Ya ce watanni takwas kenan ba su ga ko sisi a asusun bankunansu ba inda ya roki shugaban da ya kawo musu dauki
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Masu cin gajiyar shirin Gwamnatin Tarayya na N-Power sun roki Shugaba Tinubu da ya shiga lamarinsu bayan watanni takwas ba a biya su ba.
Masu cin gajiyar wadanda su ke rukunin C na 1 da 2 sun koka wa shugaban inda su ka bayyana halin kunci da su ke ciki, Legit.ng ta tattaro.
Meye 'yan N-Power su ka ce?
Sakataren yada labarai na masu cin gajiyar, Gbadebo Adesiyan ya ce rashin biyan alawus har na watanni takwas ya jefa matasan cikin mawuyacin hali.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Adesiyan ya ce babu ko daya daga cikin masu cin gajiyar shirin da ya samu alawus tun daga watan Janairun shekarar 2023 har zuwa yau.
Ya kara da cewa bisa ga bayanai da su ke samu an tabbatar musu cewa shugaban kasa, Bola Tinubu bai amince da kuma sake kudaden ba, Sahara Reporters ta tattaro.
Me ke damun 'yan N-Power?
A cewarsa:
"Yau watanni takwas kenan Gwamnatin Tarayya ba ta biya masu cin gajiyar shirin N-Power kudinsu ba.
"Wasu kuma tun watan Oktoba da Nuwamba har zuwa Disamba ba su samu ko sisin kwabo ba.
"Babu wani daga cikin masu cin gajiyar shirin N-Power da ya samu kudinsa tun watan Janairu wanda hakan ya jefa mu cikin mawuyacin hali."
Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Bayyana Yadda Ya Ji Bayan Samun N2bn Na Tinubu, Ya Tura Sako Ga Jama'a Yayin Da Su Ka Yi Martani
Matasan sun roki gwamnatin da ta kawo musu dauki ganin yadda aka nada sabuwar minista a ma'aikatar.
FG Ta Kashe N4.6bn Kan Matasan N-Power Kimanin 13,000, Sadiya
A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta sanar da kashe makudan kudade har Naira biliyan hudu da doriya kan matasa 13,000 na N-Power.
Ministar ma'aikatar, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ta bayyana hakan a bikin yaye matasa 62 da aka koyawa gyaran waya a Legas.
Asali: Legit.ng