Yan Bindiga Sun Sace Jigon Jam'iyyar APC a Jihar Kaduna
- Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaɓa da sakataren tsare-tsaren jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Kaduna
- Miyagun masu garkuwa da mutanen dai sun sace Ibrahim Kawu Yakasai ne a gidansa da ke ƙauyen Yakasai na ƙaramar hukumar Soba
- Sace sakataren na zuwa ne dai ƴan kwanaki kaɗan bayan masu garkuwa da mutanen sun sace wani kansila a yankin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace sakataren tsare-tsare na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Kaduna.
Masu garkuwa da mutanen dai sun yi awon gaba ne da Kawu Ibrahim Yakasai a cikin gidansa.
Ibrahim Kawu Yakasai wanda shi ne tsohon shugaban ƙaramar hukumar Soba ta jihar Kaduna, ya faɗa hannun miyagun ne a gidansa da ke a ƙauyen Yakasai.
Majiyoyi sun gayawa jaridar Aminiya cewa an sace sakataren ranar Juma'a da daddare bayan maharan da suka dira a ƙauyen sun yi ta harbe-harben bindiga.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sace sakataren tsare-tsaren na zuwa ne dai bayan masu garkuwa da mutane sun je har gida sun yi awon gaba da Alhaji Sabitu Ahmad, kansilan gundumar Garu ta ƙaramar hukumar Soba.
An tabbatar da aukuwar lamarin
Wani daga cikin shugabannin jam’iyyar APC na jihar Kaduna, wanda ya nemi da a sakaya sunansa, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya nuna takaicinsa kan yadda matsalar tsaro ke ta ƙara yawaita a yankin.
Ya kuma yi fatan Allah Ya kubutar da shi da sauran mutane da ke a hannun masu garkuwa da mutane cikin aminci.
Muhammad Lawal Shehu, sakataren watsa labarai na gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya tabbatar da sace Kawu Ibrahim Yakasai, inda ya ce gwamnan ya umarci jami'an tsaro su gudanar da bincike domin ganin sun ceto shi cikin aminci.
Yan Bindiga Sun Farmaki Hedikwatar Yan Sanda
A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun farmaki hedikwatar rundunar ƴan sanda ta garin Isiokolo na ƙaramar hukumar Ethiope ta Gabas a ihar Delta.
Ƴan bindigan waɗanda ake kyautata zaton ƴan daba ne sun halaka jami'in ɗan sanda guda ɗaya tare da raunata wani jami'in ɗan sanda guda ɗaya.
Asali: Legit.ng