“Buhun Shinkafa N350”: Budurwa Ta Baje Kolin Kayayyakin Da Mahaifinta Ya Siya a 1990, Farashin Ya Ba Da Mamaki

“Buhun Shinkafa N350”: Budurwa Ta Baje Kolin Kayayyakin Da Mahaifinta Ya Siya a 1990, Farashin Ya Ba Da Mamaki

  • Wata matashiya yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta baje kolin takardar siyayya da mahaifinta ya yi a 1990
  • Takardar ta nuna jerin abubuwan da zai siya a shagonsa ciki harda farashin kowani kaya a kasuwa a wancan lokacin
  • Daga jerin abubuwan, ana siyar da buhun shinkafa a kan N350, buhun garin kwaki N125 sannan ana siyar da buhun gishiri N56.50

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Yan Najeriya da dama sun yi korafin cewa abubuwa na da arha a kasar a baya, sai kuma wata budurwa yar Najeriya ta yi karin haske a kan wannan hasashe.

Adaeze Don ta wallafa wata tsohuwar takarda na siyayyar da mahaifinta ya yi a 1990 kuma farashin kayayyaki a wancan lokacin ya matukar bai wa mutane mamaki.

Farashin kayayyaki a 1990
“Buhun Shinkafa N350”: Budurwa Ta Baje Kolin Cefanensu Na 1990, Farashin Kayayyakin Ya Ba Da Mamaki Hoto: Adaeze Don
Asali: Facebook

Kayayyakin sun kasance a buhu-buhu

Kara karanta wannan

Mai POS Ta Sharbi Kuka Da Majina Yayin da Kwastoma Ya Arce Da Wayarta Bayan Ya Tura N500, Bidiyon Ya Yadu

Adaeze ta bayyana cewa kowani kaya da ke takardar an siye su ne a kan buhu-buhu, ba awo ba. Ta nuna bakin cikinta kan yadda naira ta zama bata da daraja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga jerin kayayyakin da ta wallafa a Facebook, ana siyar da buhun shinkafa kan N350, buhun garin kwaki N125, buhun kifin idde N110, sannan buhun gishiri ana siyar da shi N56.50.

Sauran kayayyaki a takardar sun hada da kiret din kwai a N25, gwangwanin man gyada N140 sannan albasa N10.50.

Yan Najeriya sun yi martani ga farashin kayayyaki a 1990

Felicia Daniel ta ce:

"Ko a wancan lokacin, mutane na korafi cewa abubuwa sun yi tsada, ku ci gaba da yin korafi kan abun da ba zai taba karewa ba."

Goodluck Chimenum Ejiowhor ya ce:

"Abubuwa a yanzu ba za su taba zama yadda suke ba a shekaru 33 da suka gabata, amma da ba zai yi muni haka ba idan da mutane masu tunani ne suke gudanar da harkokin kasar."

Kara karanta wannan

Wike Na Hawa Motar Miliyan 300 Wacce Harsashi Bai Ratsa Ta? Ministan Abuja Ya Fayyace Gaskiya

Nnenna Bella Xtopher ta ce:

"Gaba daya a kan #2,103 kacal.
"Kuma duk da haka iyayenmu a wancan lokacin suna korafi kan yadda abubuwa suke kara tsada, dubi yanzu."

Miebaka Lot ta ce:

"1990 bai yi nisa ba fa muna maganar kimanin shekaru 33 da suka gabata ne fa amma kalli banbancin Allah ya taimake mu faaaa."

Gwamnan Kano ya bai wa Fauziyya D Sulaiman mukami

A wani labari na daban, mun ji cewa mai girma gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya nada babbar mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin gajiyayyu.

Gwamnan ya nada Fauziyya D Sulaiman, yar jin kai kuma shugabar gidauniyar ' Creative helping needy foundation' a matsayin mai tallafa masa kan harkokin mabukata da gajiyayyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng