Bai Kamata Jami'ar Chicago Su Bayyana Takardu Na Ga Atiku Ba, Tinubu Ya Fada Wa Kotu

Bai Kamata Jami'ar Chicago Su Bayyana Takardu Na Ga Atiku Ba, Tinubu Ya Fada Wa Kotu

  • Shugaba Bola Tinubu ya soki shirin neman shaidar takardun makarantarshi daga jami’ar Chicago na Amurka
  • Wannan na zuwa ne bayan dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya nemi a binciko takardun Tinubu a jami’ar
  • Tinubu ya ce ganin yadda ake daf da kammala shari’ar da su ke ciki bai kamata Atiku ya bijiro da maganar takardun ba

FCT, Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya fadi dalilan da yasa bai kamata kotun Amurka ta saki takardun karatunsa ba na jami’ar Chicago.

Tinubu ya bayyana haka ne yayin da ya ke martani game da karar tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar ya shigar na bukatar shaidar karatun Tinubu daga jami’ar.

Tinubu ya bayyana dalilan kan kin amincewa da bukatar Atiku
Tinubu Ya Yi Martani Kan Bukatar Atiku Na Binciken Takardunsa. Hoto: Atiku Abubakar/Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Meye Tinubu ya ce game da bukatar Atiku?

Legit.ng ta tattaro cewa a ranar 24 ga watan Agusta, Shugaba Tinubu ya ce Atiku bai bukatar takardun karatunsa a karar wanda yanzu ta zo karshe.

Kara karanta wannan

Ana tsaka mai wuya: Abin da Tinubu ya fadawa Malaman addini kafin su tafi Nijar

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya ce lokacin da ake tsaka da karar, Atiku da lauyoyinsa ba su yi magana a kan takardun shugaban ba sai yanzu.

Tinubu ya ce tun da yanzu ana daf da kammala karar, Atiku ba shi da hurumin gabatar da wani shaida ta daban.

Har ila yau, a cikin martanin Tinubu, ya ce wani daga cikin magatakardan jami’ar ya yi kuskure wurin rubuta shekaru kamar yadda makarantar ta yi inda hakan ya kawo cece-kuce.

Me yasa Atiku ke bukatar takardun Tinubu?

Atiku tun farko ya bukaci jami’ar ta gabatar takardun karatun Tinubu wanda hakan ya ke ganin zai taimaka wurin karar da su ka shigar a gaban kotun sauraran kararrakin zabe, cewar TheCable.

An samu rikita-rikita yayin da Tinubu ya gabatar da shaidar karatunsa ga hukumar zabe mai zaman kanta inda aka ga mace ce ke dauke da sunan Bola Tinubu wacce aka Haifa a ranar 29 ga watan Maris 1954.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar LP Ta Rasa Kujerar Majalisa, Kotu Ta ba Mutumin Tinubu Nasara a APC

Jami'ar Chicago Ta Amince Ta Saki Takardun Karatun Tinubu

A wani labarin, da alamu shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai shiga damuwa yayin da jami'ar Chicago ta amince ta bayyana takardun karatunsa lokacin da yake dalibi a jami'ar.

Jam'iyyar PDP, a cikin wani rubutu da ta yi a ranar Alhamis, 24 ga watan Agusta, ta yi ikirarin cewa jami'ar ta amince ta ba kotu takardun karatun Shugaba Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.