Minista Ya Shiga Aiki Gadan-Gadan, Ya Yi Wa ‘Yan Kwangila Kaca-Kaca a Abuja

Minista Ya Shiga Aiki Gadan-Gadan, Ya Yi Wa ‘Yan Kwangila Kaca-Kaca a Abuja

  • Sabon Minista, David Umahi ya fara zagaye domin ganin ayyukan tituna da ake yi a fadin Najeriya
  • A makon nan tsohon gwamnan ya shiga ofis, zai jagoranci ma’aikatar ayyuka a gwamnatin tarayya
  • Umahi bai ya koka kan aikin titin Abuja-Lokoja, ya ce dole ayi aiki da kyau idan har an karbi kudi

Abuja – Sabon ministan ayyuka, David Umahi bai ji dadin kyawun aikin titin Abuja-Lokoja ba, bai gamsu da nagartar kwangilar ba.

Punch ta ce Sanata David Umahi ya yi Allah-wadai da abin da ya gani da idanunsa a yayin da ya ziyarci aikin titin da gwamnati ta ke yi.

Ministan ya hadu da ‘yan kwangilar ranar Laraba a Abuja, ya nuna rashin na’am dinsa da yadda ya samu wadannan kwangilar hanyoyi.

gwamna
David Umahi a lokacin ana aiki Hoto: @FrancisNwaze1
Asali: Twitter

Bayan an rantsar da shi a farkon makon, Umahi ya duba titin Abuja-Lokoja da na Lokoja-Benin, babu abin yabawa a wajen ministan.

Kara karanta wannan

Sabon Minista Ya Fadi Sanatan APC da Ya Zama Silar Samun Mukaminsa a Gwamnati

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Na duba ayyuka kusan takwas a kan titunan Abuja zuwa Lokoja kuma na yi bakin ciki da irin abubuwan da na gani.
Ta ya za ka karbi kudin wani abu kuma ba za ka yi da kyau ba? Ku na tsoron Ubangiji kuwa? Dole ne mu yi aikin mutane.”

- David Umahi

Sai an gyara aikin Abuja-Lokoja

Business Day ta ce ministan ya zargi ‘yan kwangilar da jawo karancin abinci a garin Abuja, ya ce babu tanadin da aka yi domin damina.

Umahi wanda asalinsa injiniya ne, yake cewa bincikensa ya nuna masa babu yadda za ayi idan ana neman agajin gaggawa na zuwa asibiti.

Ministan ya tunawa masu wannan aiki cewa dole a shimifida hanyoyi masu kyau domin shugaban kasa ya cika alkawuran da ya dauka.

"Na yi aiki a Ebonyi" - Minista

Kara karanta wannan

Wike Ya Bai Wa Yan Kwangila Wata 8 Su Kammala Aikin Layin Dogo Na Zamani a Abuja

Da aka yi hira da tsohon gwamnan a tashar Channels, ya bada labarin yadda ya gina titin kilomita 3, 500 a Ebonyi wanda bai bukatar gyara.

"Na yi titin kilomita 3, 500 a Ebonyi, kuma bai bukatar gyara. Idan za a shekara 50, ba za a gyara shi ba.
Na bukaci a dawo da takardun da mu ka aikawa BPP. Dole mu fito da sababbin hanyoyi gina tituna ta yadda za su dace da yanayinmu."

- David Umahi

Tinubu ya bar tarihi

Ku na da labari Injiniya Abubakar Momoh ya zama Sabon ministan Neja-Delta, lamarin da ya ba shi kan shi mamaki da aka sanar.

A tarihi ba a taba samun mutumin Edo da ya rike ma’aikatar harkokin Neja-Delta ba, sannan mutumin Kudu, ya zama Minista na Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng