Jami'in DSS Ya Soka Wa Dattijo Wuka A Kwankwaso Kan Naira Dubu 3 A Jihar Osun
- Wani jami'in hukumar DSS ya daba wa wani dattijo wuka a kwankwaso kan Naira dubu uku a birnin Osogbo na jihar Osun
- Dattijon mai shekaru 62, Omoshola Oludele ya gamu da tsautsayin ne yayin da ya je tattara kudin wutar lantarki a gidajen haya da ya ke kula da su
- Jami'in DSS din ya ce ba zai biya kudin wutar ba wanda hakan ya jawo rigima da yamutsi da har ya soka wa dattijon wuka
Jihar Osun - Ana zargin wani jami'in Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da soka wa wani dattijo wuka kan Naira dubu uku a jihar Osun.
Wanda ake zargin ya soka wa dattijo Omoshola Oludele mai shekaru 62 wuka a kwankwaso.
Meye ake zargin jami'in DSS din da shi?
Wata majiya ta tabbatar da cewa dattijon shi ke kula gida hayan da jami'in DSS din ke zaune yayin da bukace shi ya biya kudin wuta Naira dubu uku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan shi ya jawo takaddama a tsakaninsu inda jami'in ya ce ba zai biya ba wanda har ta kai ga caka masa wuka.
Jami'in DSS din na haya ne a unguwar Tinumola da ke birnin Osogbo na jihar Osun.
Shaidu sun ce dattijon wanda shi ne mai kula da gidajen hayan ya je ne don tattara kudaden wutar lantarki a gidan lokacin da abin ya faru.
Wani ganau ya tabbatarwa Aminiya cewa jami'in DSS din ya ji wa dattijon, Mista Oludele mummunan rauni a kwankwaso.
Meye mutane su ka ce kan jami'in DSS?
Tosin Moronkola ya ce an garzaya da Oludele asibiti don ba shi kulawar gaggawa.
Jama'ar yankin sun bukaci hukumomi su yi bincike tare da daukar mataki a kan jami'in DSS din don dakile faruwar hakan a gaba, cewar Daily Trust.
Wike Ya Fasa Kwai, Ya Bayyana Cewa Gwamnonin PDP 10 Sun Gabatarwa Tinubu Da Sunaye Don Ba Su Mukamai
Wani babban jami'i a Hukumar ta DSS ya shaidawa 'yan jaridu cewa hukumar za ta yi kwakkwaran bincike tare da hukunta wanda ake zargi dai-dai da laifin da ya aikata.
DSS Ta Gayyaci Dan Takarar Gwamnan APC A Kogi
A wani labarin, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS ta gayyaci dan takarar gwamna a jihar Kogi karkashin jami'iyyar APC, Ahmed Ododo don amsa tambayoyi.
Hukumar ta gayyaci Ododo ne saboda wasu korafe-korafe da 'yan jam'iyyar adawa su ka gabatar a kansa.
Asali: Legit.ng