Chajin Kudin POS Ya Sauka Da 90% Bayan Hukuncin Kotun Koli Yayin da CBN Ke Jiran Shawarar Bangaren Shari’a

Chajin Kudin POS Ya Sauka Da 90% Bayan Hukuncin Kotun Koli Yayin da CBN Ke Jiran Shawarar Bangaren Shari’a

  • Masu POS sun fara karbar tsoffin takardun naira bayan hukuncin da kotun koli ta zartar
  • Hukuncin kotun ya karya chajin POS da kaso 90 cikin dari yayin da tsabar kudi ya fara wadata
  • Sai dai kuma, CBN ya ce yana jiran shawarar shari'a kafin ya yanke shawara kan ko ya aiwatar da hukuncin kotun koli

An samu ruguzowar chaji da masu POS ke yi yayin cire kudi biyo bayan hukuncin kotun koli na ranar Juma'a, 3 ga watan Maris din 2023 cewa a ci gaba da amfani da tsoffin kudi yan N200, N500 da N1000 har zuwa 31 ga watan Disambar 2023.

Masu dauko rahoto daga jama'a sun nuna cewa masu POS sun fara rage kudin chaji yayin cire kudi da kaso 90 cikin dari yayin da bankuna suka gabatarwa kwastamominsu da karin tsabar kudi.

Kara karanta wannan

Yan Kasuwa Da Direbobi Na Cigaba Da Kin Karbar Tsohon Kudi Duk Da Umarnin Kotun Koli

Wuraren cire kudi ta POS
Chajin Kudin POS Ya Sauka Da 90% Bayan Hukuncin Kotun Koli Yayin da CBN Ke Jiran Shawarar Bangaren Shari’a Hoto: PIUS UTOMI
Asali: Getty Images

Bankuna sun fito da karin tsabar kudi

Hukuncin babbar kotun ne ya haddasa karyewar chajin da masu POS ke yi yayin da jama'a ke iya samun kudi a kan kanta da ATM din bankuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu kudi a banki sun ce duk da dogon layi da ke bankuna, sun samu damar cire kudi kasancewar bankuna sun cika ATM dinsu da tsaba.

Hakazalika, wasu masu POS sun ce sun fara ganin ragomar masu zuwa cire kudi bayan zaben shugaban kasa na 2023 kasancewar an samu sauki wajen rashin wadatuwar kudi.

Masu POS sun rage kudin chaji

Wasu masu POS a Lagas sun ce sun fara karbar tsoffin kudi yayin tura sakon kudi tunda an ce har yanzu halastattu ne kuma yanzu suna da isasshen tsaba na gudanar da harkokinsu.

"Yanzu ina chajin N300 kan N10,000. Kafin hukuncin kotun koli, da ana chajin N2000 kan kowani N10,000 saboda samun tsoffi da sabbin N200 yana da matukar wahala kuma ina biyan kudi da yawa a kansu," inji wani mai POS.

Kara karanta wannan

Ci gaba da kashe tsoffin Naira: Bankuna sun yi magana bayan hukuncin kotun koli

Masu POS sun ce hukuncin kotun koli zai farfado da kasuwancinsu kasancewar za a samu karin tsaba domin yawancin masu aikin sun rufe saboda rashin kudi.

Wasu masu POS na chajin N300 da N500 kan kowani N1000 da za a tura saboda wasu yan kasuwa da ke da tsoffin kudi suna fitowa da shi yanzu.

CBN na jiran shawarar shari'a

A halin da ake ciki, jaridar Vanguard ta rahoto cewa babban bankin Najeriya (CBN) na jiran shawarar bangaren shari'a game da hukuncin kotun koli kan manufar sauya kudi.

A cewar jaridar, wani babban jami'in babban bankin ya ce CBN za bayyana matsayinsa nan ba da jimawa ba amma yana jiran shawarar masu shari'a, daga ofishi Atoni Janar na tarayya.

CBN ya bayyana cewa bai da abun cewa game da hukuncin kotun kolin, wanda yasa ake hasashen cewa ba lallai ne ya bi umurnin kotun koli na barin tsoffi kudi su ci gaba da aiki har zuwa 31 ga watan Disambar shekarar nan ba.

A wani labari na daban, mun ji a baya cewa wani matashi ya shiga hannun yan sanda bayan samunsa da aka yi da bandir-bandir din kudi yan N500 na bogi

Asali: Legit.ng

Online view pixel