Emefiele Ya Na Neman Yadda Zai Sasanta da Gwamnati Kan ‘Satar’ Naira Biliyan 6

Emefiele Ya Na Neman Yadda Zai Sasanta da Gwamnati Kan ‘Satar’ Naira Biliyan 6

  • Da alama an kusa zuwa karshen shari’ar da ake bugawa tsakanin Godwin Emefiele da gwamnati
  • Tsohon gwamnan babban banki na CBN ya kawo shawarar a nemi yadda za a sasanta a wajen kotu
  • Idan aka yi haka, gwamnati za ta janye karar da ta shigar sai wanda ake tuhuma zai bada hadin-kai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Sau biyu a jere kenan ana neman a gurfanar da dakataccen gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele a gaban kotu, amma abin ya gagara.

Wasu majiyoyi sun shaidawa The Cable ana ta ja-baya da karar ne a sakamakon matsayar da aka cin ma na yin sulhu ba tare da an je kotu ba.

Alamu na nuna wanda ake tuhuma da laifi, Godwin Emefiele, ya amince ya sasanta da gwamnatin tarayya domin yafe masa zargin da ke wuyansa.

Kara karanta wannan

“Ina Dalili”: Suka, Martani Kan Nadin Hadimai Mata 131 Da Gwamnan Arewa Ya Yi

CBN Emefiele
An dakatar da Godwin Emefiele daga CBN Hoto:@Cenbank
Asali: Twitter

Akwai zargi 20 da ake yi wa Emefiele a babban kotun tarayya da ke Abuja, amma har zuwa yanzu ba a gurfanar da shi domin a fara yin shari’a ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daily Sun ta ce ko a zaman karshe da aka yi a kotun, an dakatar da sauraron shari’ar ne bayan da tsohon gwamnan bankin ya amince da ayi hakan.

Majiyar ta ce za a sanar da lokaci na dabam da alkali zai soma sauraron shari’ar tun da aka gaza gurfanar da wanda ake kara a tsakiyar makon nan.

Ana kyautata zaton Emefiele da abokiyar tuhumarsa, Sa'adat Yaro duk sun amince su sasanta da lauyoyin gwamnatin tarayya kafin a shiga kotu.

Lauya mai bada kariya Kehinde Akinlolu

Da aka zanta da lauyan tsohon gwamnan babban bankin kasar, Kehinde Akinlolu SAN, ya nuna abubuwa sun canza a karar da ake yi a babban kotun.

Kara karanta wannan

Wike Ya Jero Mutanen Da Zai Cusa Kafar Wando Daya Da Su Bayan Zama Minista

Lauyan ya ke cewa watakila a kai maganar zuwa wajen mai shari’a Husseini Baba Yusuf.

Godwin Emefiele ya kawo maganar

Wani lauya a bangaren masu kara, ya shaida cewa tsohon shugaban na CBN ya kawo maganar a sasanta da mahukunta, Vanguard ta fitar da rahoton.

Dokar ACJA ta halattawa wanda ake zargi da laifi ya nemi a yanke hukunci mara tsauri ko ayi watsi da zargin da ake yi masa idan ya bada hadin-kai.

Wanda ake kara zai bukaci a janye maganar daga kotu, sai a sasanta ta yadda za a samu mafita ba tare da an sha wahalar kashe kudi da bata lokaci ba.

Hannatu Musa Musawa v CBN

Babban bankin CBN zai yi bincike kan zargin likin kudi da Ministar al'adu, Hannatu Musa Musawa ta rika yi a Abuja wajen bikin da aka shirya mata.

Ku na da labari cewa a dokar kasar nan, za a iya daure wanda aka samu ya na wulakanta Naira, wannan laifi zai iya jawo zaman gidan kurkuku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng