Bayan Shekaru 13 A Rufe Saboda Tsaro, NYSC Ta Sake Bude Sansanin Bada Horaswa Na Borno

Bayan Shekaru 13 A Rufe Saboda Tsaro, NYSC Ta Sake Bude Sansanin Bada Horaswa Na Borno

  • An bude sansanin ba da horo na Hukumar NYSC bayan shafe shekaru 13 a rufe a Maiduguri da ke jihar Borno
  • Wannan na zuwa ne bayan samun tabbacin zaman lafiya yayin da rundunar soji ke kara samun nasara kan 'yan Boko Haram
  • Rundunar sojin kasar ta bayyana hakan a matsayin wata nasara da rundunar 'Operation Hadin Kai' ke samu kan mayakan Boko Haram

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Borno - Hukumar Matasa Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC) ta samu nasarar bude sansanin ba da horaswa da ke Maiduguri a jihar Borno.

Wannan na zuwa bayan shafe shekaru 13 da kulle sansanin saboda rashin tsaro, Legit.ng ta tattaro.

NYSC ta sake bude sansanin ba da horaswa da ke Borno
Bayan Shekaru 13 A Rufe, NYSC Ta Bude Sansanin Bada Horaswa A Borno. Hoto: @HQNigerianArmy.
Asali: Twitter

Menene dalilin rufe sansanin NYSC?

An rufe sansanin ba da horaswar ne shekarar 2011 saboda hare-haren 'yan Boko Haram da ya yi kamari.

Kara karanta wannan

Musulmai Sun Yi Wa Direban Jirgin Sojojin Da ‘Yan Ta’adda Su Ka Kashe Sallar Jana’iza

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bude sansanin ne a jiya Talata 22 ga watan Agusta yayin da rundunar sojin kasar ta yabawa jami'anta saboda kokarin yaki da Boko Haram.

Rundunar ta ce bude sansanin ya tabbatar da nasarar da rundunar ke samu kan mayakan Boko Haram.

Ta ce samun zaman lafiya ne ya jawo bude sansanin wanda rundunar soji ta 'Operation Hadin Kai' (OPHK) ke jagorantar gumurzun yaki da 'yan ta'adda.

Jihar Borno ta sha fama da hare-haren mayakan Boko Haram da ya yi sanadin rasa rayuka da dama musamman a kauyuka.

Meye martanin sojoji kan bude sansanin NYSC?

Rundunar ta bayyana haka ne shafinta na Twitter kamar haka:

"An bude sansanin ba da horo na Hukumar NYSC da ke Maiduguri a jihar Borno a jiya Talata 22 ga watan Agusta bayan shekaru 13 a kulle saboda ta'addanci.

Kara karanta wannan

Diesani Alison-Madueke: Ana Tuhumar Tsohuwar Ministan Jonathan Da Cin Hanci, Yan Sandan Birtaniya Sun Yi Bayani

"Bude sansanin ya nuna tabbacin samun zaman lafiya yayin da rundunar 'Operation Hadin Kai' (OPHK) ke kara samun nasara a kan mayakan Boko Haram.

'Yan Ta'adda Sun Sace Masu Bautar Kasa 8 A Jihar Zamfara

A wani labarin, 'yan bindiga sun sace wasu matasa masu yi wa kasa hidima, NYSC su guda takwas a jihar Zamfara.

'Yan bautar kasar da lamarin ya shafa suna cikin wata motar Bas AKTC kuma sun fito ne daga birnin Uyo ta jihar Akwa Ibom.

Bayanai sun tattaro cewa matasan na shirin shiga jihar Zamfara ne don hidimtawa kasa da ya zama wajibi yayin da su ka ci karo da 'yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.