Matawalle Ya Yi Martani Ga Masu Korafi Kan Mukaminsu Na Minista, Ya Sha Alwashin Kawo Sauyi A Tsaron Kasar

Matawalle Ya Yi Martani Ga Masu Korafi Kan Mukaminsu Na Minista, Ya Sha Alwashin Kawo Sauyi A Tsaron Kasar

  • Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya soki masu cece-kuce kan nadinsu ministocin tsaro
  • Bello ya bayyana haka ne cikin wani faifan bidiyon da ya karade kafofin sadarwa inda ya ce za su kawo sauyi
  • Matawalle ya kalubalanci masu korafin da cewa ba su san komai ba a kan harkokin tsaron kasar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Zamfara – Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi martani ga masu cewa ba zai kawo sauyi a harkokin tsaro ba.

Matawalle ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo inda ya ke raddi ga masu musu isgili cewa ba za su iya rike ma’aikatar ba.

Matawalle ya ba da tabbacin za su kawo sauyi a ma'aikatar tsaro
Matawalle Ya Sha Alwashin Bai Wa Marada Kunya Don Kawo Sauyi A Tsaron Kasar. Hoto: Badaru Abubakar, Bello Matawalle.
Asali: Facebook

Meye 'yan Najeriya ke cewa kan Matawalle?

Tun bayan raba ma’aikatu ga ministocin da Shugaba Tinubu ya yi, mutane su ke cece-kuce kan ma’aikatar tsaro da aka ba wa Badaru Abubakar da Bello Matawalle.

Kara karanta wannan

Ministocin Tsaro: Badaru da Matawalle Sun Ɗauki Alkawari, Sun Faɗi Lokacin da Za'a Ga Sauyi a Tsaron Ƙasa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

‘Yan Najeriya sun nuna shakku kan ingancinsu da kuma sauyi da za su kawo ganin yadda kasar ke fama da matsalar tsaro ta ko wani bangare.

A cikin faifan bidiyon, Matawalle ya ce mutanen da su ke magana akai yawanci ba su ma san menene tsaro din da ake magana ba.

Ya ce:

“Na ji ana ta korafi cewa da ni da dan uwana Badaru ba za mu iya zama ministocin tsaro ba, wadanda ke maganan ba su san menene tsaro ba.
“Domin za ka iya haifar yaro amma ya zo ya fi ka kwazo da hikima da ilimi na gudanar da abu.”

Ya kara da cewa shi matsayi abu ne da ka san za ka iya ko ba za ka iyaba ko kuma ka na da kwarin gwiwar yin haka, TRT Hausa ta tattaro.

Kara karanta wannan

Wike Ya Jero Mutanen Da Zai Cusa Kafar Wando Daya Da Su Bayan Zama Minista

Wane martani Matawalle ya yi?

A cikin faifan bidiyon, Matawalle ya ce:

“Lokacin da na ke gwamna babu hanyar da ba mu bi ba don dakile harkar tsaro, sai da aka yi kwanaki 100 ba a taba kowa ba, sannan aka sake watanni tara ba a taba kowa ba.
“Duk matakan da na ke dauka don dakile rashin tsaro a Zamfara, sai da na yi wasu su ke kwaikwayo.”

Tun bayan nadin ministocin musamman na tsaro mutane ke ta korafin cewa ba a ajiye kwarya a gurbinta ba, ganin yadda aka nada Matawalle da Badaru a matsayin ministocin tsaro, Premium Times ta ruwaito.

Nadin Matawalle Ya Sa 'Yan Ta'adda Shiga Rudani, Kaura

A wani labarin, hadimin karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, Anas Kaura ya ce daga nadin Matawalle 'yan ta'adda su ka shiga taitayinsu.

Kaura ya bayyana haka ne yayin da ake ta korafi kan mukamin minista da aka ba wa tsohon gwamnan Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.