Jami'an Amotekun Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 3 Yayin Karban Kudin Fansa a Jihar Ondo
- Jami'an tsaro na Amotekun sun cafke masu garkuwa da mutane uku yayin karɓar kudin fansa
- Lamarin ya faru ne bayan sace wani bawan Allah da masu garkuwar suka yi a gidansa yayin sallar Magriba
- Jami'an sun kuma yi nasarar kamo sauran abokan aikin mutane ukun da suka kama da farko
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Akure, jihar Ondo - Jami'an hukumar tsaro ta jihar Ondo, da ake kira da Amotekun, sun yi nasarar cafke mutane 3 da ake zargi da laifin garkuwa da mutane a jihar.
Kwamandan Amotekun na Ondo, Adentunji Adeleye ne ya bayyana hakan a yayin da yake gabatar da waɗanda aka kama da ƙarin wasu 22 masu aikata wasu laifukan a Akure babban birnin jihar.
Yadda aka kama masu garkuwa da mutane 3 a Ondo
Adeleye ya bayyana cewa masu garkuwan sun ɗauki wani mai suna Audu Bello a gidansa da ke ƙaramar hukumar Akoko ta Arewa maso Yamma da misalin ƙarfe bakwai na yamma.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce sun tarar da shi yana sallah, inda sai da suka lakaɗa ma sa duka kafin bisani su tafi da shi zuwa cikin jeji kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.
Ya ƙara da cewa jami'ansu sun yi basaja a matsayin 'yan uwan mutumin da aka sace da nufin sun zo kawo kuɗin fansa, inda a yayin bayar da kuɗin ne suka cafke mutane uku.
Adeleye ya kuma bayyana cewa bayanan da aka samu daga wurin mutanen uku ne suka taimaka aka kamo ƙarin wasu shida daga cikinsu.
“Gari na yi ta sha hannun masu garkuwa da mutane” , Bello
Da yake zantawa da manema labarai, Audu Bello ya ce masu garkuwa da mutanen sun same shi yana sallar Magriba a gidansa da misalin ƙarfe bakwai na yamma.
Ya ce sun zo ɗauke da manyan bindigu inda suka lakaɗa ma sa duka a gidan na sa kafin daga bisani suka tasa ƙeyarsa zuwa cikin jeji.
Ya ce garin kwaki ɗan kaɗan suka riƙa ba shi yana sha a zaman kwanaki biyar da ya yi a hannunsu kafin jami'an Amotekun su yi nasarar cetonsa kamar yadda The Guardian ta wallafa.
'Yan ta'adda na shirin kai wa jirgin ƙasan Abuja-Kaduna hari
Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan bayanan da jami'an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) suka fitar na shirin sake kai hari kan jirgin ƙasan da ke jigilar mutane daga Kaduna zuwa Abuja.
Hukumar DSS ta aikewa hukumar kula da jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC) wasiƙa, inda ta ankarar da ita kan shirin da 'yan ta'addan ke yi.
Asali: Legit.ng