Bola Tinubu Ya Shiga Ganawar Sirri da Ribadu, Manyan ECOWAS a kan Yaki da Nijar

Bola Tinubu Ya Shiga Ganawar Sirri da Ribadu, Manyan ECOWAS a kan Yaki da Nijar

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa a kan sha’anin tsaro da jagororin kungiyar ECOWAS
  • Tun da aka kifar da Mohammed Bazoum, Shugaban Najeriya da ECOWAS su ke ta fadi-tashi a Afrika
  • Yanzu haka Dr Omar Touray da Abdulsalami Abubakar su na Aso Rock, sun hadu da Shugaba Tinubu

Abuja - Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yanzu haka ya na ganawa da wasu a cikin masu ruwa da tsaki na kungiyar ECOWAS.

Makasudin tattaunawar ba za ta rasa alaka da rikicin da ake neman shiga a yammacin Afrika a sakamakon juyin mulki a Nijar ba.

Vanguard a rahoton da ta fitar ta ce ana zaman ne domin ganin yadda za a shawo kan matsalar da ake ciki tun bayan kifar da farar hula.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a taron ECOWAS Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

ECOWAS ba ta tare da Sojojin Nijar

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: Da Gaske Janar Tchiani Ya Kira Gwamnatin Tinubu Da haramtacciya? Gaskiya Ta Yi Halinta

Kungiyar ECOWAS ta kasashen yammacin Afrika ta na son ganin an koma mulkin farar hula a Nijar da ke da iyaka da kasar Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban hukumar ECOWAS, Dr Omar Touray da shugaban tawagar da aka tura zuwa Nijar, Abdulsalami Abubakar su na wajen taron.

Mai ba shugaban Najeriya shawara a kan harkar tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya na cikin wadanda aka sa labule da shi domin a tattauna.

Rahoton Abdulsalami Abubakar

Da Janar Abdulsalami Abubakar su ka hadu da sojojin tawaye a Niamey, sam bai bari ya shaidawa duniya yadda zamansu ya kaya ba.

Tsohon shugaban Najeriyan ya ki cewa uffan a jamhuriyyar Nijar, ya ce Mai girma Bola Tinubu ne zai fara jin yadda aka yi tukuna.

Tattaunawar ta na zuwa ne yayin da mutane har da Nasir El-Rufai su ke ganin alakar Arewacin Najeriya da Nijar ta fi karfin a jawo yaki.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Yayin Da ECOWAS, Nijar Su Ka Gaza Samun Daidaito, Fafaroma Francis Ya Shiga Tsakani

An kifar da gwamnati a Nijar

Mai girma Bola Tinubu shi ne shugaban ECOWAS, karbar wannan kujera ke da wuya, sojoji su ka shirya juyin mulki a makwabtan na sa.

A makon jiya Janar Abdourahamane Tchiani ya yi wa 'Yan jahmuriyyar Nijar jawabi a gidajen talabijin, ya nuna sai 2026 za su bar mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng