Elon Musk Ya Samu Dala Biliyan 11 Cikin Dare Yayin Da Dangote Ya Yi Asarar Biliyan 43 A Kwana Daya
- Shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk, ya dawo da karfinsa inda ya samu dala biliyan 11 a dare daya
- Wannan ci gaban ya kasance ne sakamakon karin hannun jari da kamfanin motoci masu amfani da lantarki, Tesla ta samu
- Sabanin haka, attajirin da ya fi kowa kudi a Najeriya, Aliko Dangote, ya yi asarar naira biliyan 43.3 a ranar Litinin, 21 ga Agusta, 2023
Shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk ya shawo kan asarar da aka kwashe makonni ana tafkawa a kasuwannin hannayen jari na duniya inda ya samu sama da dala biliyan 11 a dare daya.
Mamallakin kamfanin na X, wanda arzikinsa ya ragu bayan ya rufe da dala biliyan 200, ya sake dawowa kan kafafunsa yayin da hannayen jarin kamfanin Tesla suka farfado.
Kamfanin Tesla ya sake farfadowa yayin da sauran attajirai suka samu riba mai yawa
A ranar Litinin, 21 ga watan Agustan 2023, an siyar da hannayen jarin Tesla kan $231.28 kowanne, inda ya farfado da kashi 7.33 daga lokacin da ya fada jan layi yayin da yan kasuwa suka karkata ga wani wajen don samun riba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Musk yana neman hanyar tatsar kudi a da yawan fasalin manhajar X, wanda a baya ake kira Twitter, kuma ana tunanin shine mutum na farko da zai taba mallakar kudi dala tiriliyan 1.
Ga dukkan alamu Musk na da jan aiki a gabansa a mafarkin da yake yi na son zama mutum na farko da zai mallaki dala tiriliyan 1 yayin da kasuwar hannayen jari na duniya ke ci gaba da canzawa.
A cewar Bloomberg, sauran attajirai sun samu kari sosai a darajar arzikinsu a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta.
Dangote ya yi asara yayin da ya yi jinkiri wajen kaddamar da matatar Dangote
Mai kudin Najeriya, Aliko Dangote, ya samu ragi a arzikinsa da naira biliyan 43.4 a kwana daya yayin da hannun jarin kamfanin simintinsa ya fadi warwas.
Yan kasuwa a kasuwar canjin Najeriya sun fi mayar da hankali ne a kan hada-hadar hannayen jarin bankuna yayin da kasuwar ke ta rawa kan labarin nada sabbin ministoci da shugaban Najeriyan ya yi.
Mai kudin Afrika ya yi alkawari cewa matatar mansa mai karfin 650,000bpd, zai fara aiki a watan jiya amma da alama an dage shi zuwa wani lokaci da ba a sani ba yayin da yan Najeriya ke ci gaba da fama da hauhawan farashin mai.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi umurnin dakatar da karin farashin man fetur.
A kwanaki Dangote ya koma matsayinsa a matsayin mai kudin Afrika bayan dan Afrika ta Kudu Johann Rupert ya haye shi.
Shugaban rukunin kamfanonin na Dangote ya kwashe shekaru 12 a wannan matsayi har sai da Rupert ya yi masa juyin mulki a takaice sakamakon faduwar darajar kudin Najeriya, Naira.
Dangote Ya Sake Hayewa Teburin Masu Kudin Nahiyar Afirka
A wani labarin, mun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya sake karbar matsayinsa na wanda ya fi kowa kudi a Nahiyar Afirka bayan doke Johann Rupert.
Dangote ya koma mataki na daya wata daya bayan ya rasa matsayin kan sabbin tsare-tsare na Babban Bankin Najeriya, CBN.
Asali: Legit.ng