Ministoci: Watakila Wike ya Karbe Takardun Filaye, Ruguza Gine-Gine 6,000 a Abuja
- Mazauna Abuja za su tsure bayan jin labarin yadda Ministan Abuja, Nyesom Wike ya shiga ofis
- Tsohon Gwamnan ya yi alkawarin dawo da babban birnin kan asalin tsarin ginin da aka yi masa
- Maido tsarin zai jawo mutane su rasa kadarorinsu, kuma gwamnatin tarayya ta ruguza gine-gine
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Akwai yiwuwar gwamnatin tarayya ta shiga unguwanni akalla 30 kuma ta sauke gine-ginen da sun fi 6, 000 idan ana so a gyara Abuja.
Wani rahoton da Punch ta fitar ya bayyana cewa muddin ana sha’awar dawo da tsarin birnin tarayya, za a rugurguza gine-gine masu dinbin yawa.
Jim kadan bayan rantsar da Nyesom Wike a matsayin ministan babban birnin, ya tabbatar da cewa zai yi rugu-rugu da duk ginin da ya sabawa tsari.
Kamar yadda aka yi tsakanin 2003 da 2007, Wike ya shaida zai kai gini kasa ko da na babban mutum ne, ya nuna har jakadun kasar ba su tsira ba.
Cire Tallafi: Sauki Ya Zo Yayin Da Tinubu Ya Shirya Siyar Da Litar Gas Naira 250 Madadin Fetur, Ya Tura Bukata Ga 'Yan Najeriya
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wasu unguwannin Abuja abin zai fi shafa?
Binciken da jaridar ta gudanar ya nuna wuraren da gyare-gyaren sabon ministan zai shafa za su hada da Apo Mechanic Village, Byanzhin da Dawaki.
‘Yan unguwannin Lugbe, Dei Dei, Durumi, Dutse, Garki, Garki Village, Gishiri, Gwagwalape, Idu, Jabi, Kado Village da Karmo su na cikin matsala.
Ragowar su ne: Karshi, Karu, Katampe, Ketti, Kpaduma, Kabusa, Kpana Village, Kubwa, Lokogoma, Mabushi, Mpape, Nyanya da kuma Piya Kasa.
FCTA: Gidaje 6, 000 ake magana
Idan aka yi nazari da kyau, za a fahimci gine-ginen da ministan zai iya saukewa kasa za su doshi 6, 000. A ciki har da kangon da su ka dade ba a gina ba.
Tun a shekarar 2022 wani rahoto na hukumar FCTA ya nuna akwai gidaje akalla 6, 000 da aka yi watsi da su, ana iya karbe takardunsu ko a rusa su.
Mutanen Abuja za su tsure
Adadin gine-ginen da ke cikin barazana za su kara yawa da zarar an hada gine-ginen da aka yi a wasu lunguga da kauyuka a kewayen babban birnin.
Wadanda su ka saye filaye a hannun ‘yan gari za su iya asarar dukiyarsu domin cinikin ya saba doka wanda hakan ya jefa mazauna Abuja a dar-dar.
'Yan adawa za su hada-kai
Ku na da labari manyan ‘Yan takaran Shugaban kasa a zaben 2023 su na so su yi wa jam’iyyar APC taron dangi, watakila PDP, LP da NNPP su hada-kai.
Dama can Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso sun yi takara a jam’iyyar PDP tare a 2019, Muhammadu Buhari ya doke su gaba daya a APC.
Asali: Legit.ng