Wike Ya Fasa Kwai, Ya Bayyana Cewa Gwamnonin PDP 10 Sun Gabatarwa Tinubu Da Sunaye Don Ba Su Mukamai

Wike Ya Fasa Kwai, Ya Bayyana Cewa Gwamnonin PDP 10 Sun Gabatarwa Tinubu Da Sunaye Don Ba Su Mukamai

  • Nyesom Wike, sabon ministan Abuja da aka rantsar ya bayyana cewa akalla gwamnonin PDP 10 ne suka gabatarwa Shugaban kasa Bola Tinubu sunaye don nada su mukamai
  • Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya ce gwamnonin PDP 10 sun amsa tayin Shugaban kasa Tinubu na gabatar da sunayen wadanda za a nada mukamai, amma shi kadai aka taso a gaba
  • Wike ya ce wadanda ke kira ga dakatar da shi a PDP 'yan rawan nanaye' ne yayin da ya bukaci jama'a da su yi watsi da su sannan su fuskanci zahirin gaskiya

Abuja - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya kira wadanda ke kira ga dakatar da shi daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin "yan rawan nanaye".

Wike, wanda ya rike mukamin gwamnan jihar Ribas sau biyu a karkashin jam'iyyar PDP ya yi martanin ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan rantsar da shi a matsayin minista a karkashin gwamnatin jam'iyyar APC a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Sabon Rikici Ya Kunno Kai a PDP Yayin da Babban Jigon Jam’iyyar Ya Koma APC, An Fadi Dalili

Wike ya ce gwamnonin PDP 10 duk sun gabatarwa Tinubu da sunayen mutane da za a nada mukami
Wike Ya Fasa Kwai, Ya Bayyana Cewa Gwamnonin PDP 10 Sun Gabatarwa Tinubu Da Sunaye Don Ba Su Mukamai Hoto: Nyesom Wike
Asali: Twitter

A taron manema labaran, tsohon gwamnan na PDP ya bayyana cewa 10 daga cikin gwamnonin PDP sun gabatarwa Shugaban kasa Bola Tinubu da sunayen mutane sannan ya tambayi dalilin da yasa shi kadai ake caccaka.

Wani bangare na jawabinsa na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ina yin dariya ga yan rawan nanayen da ke PDP wandanda ke tattauna batun dakatar da-mutane masu ban dariya. Ku share su sannan mu mayar da hankali kan batu na gaskiya. Babu wani gwamnan PDP da bai zabarwa Shugaban kasa wani ba. Gaba dayansu sun zabi mutum gona-goma kowannensu."

Yadda shugabannin PDP suka marawa mukamina baya

Wike ya kuma bayyana cewa ya sanar da shugabannin PDP na kasa, yanki da jiha kafin ya yanke shawarar karbar mukamin da shugaban kasa Tinubu ya yi masa tayi.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Gwangwaje Sojojin Da Suka Ji Rauni Da Kyautar Kudi Masu Yawan Gaske

Ya ci gaba da cewar ya kuma tuntubi shugabannin marasa rinjaye na majalisar wakilai, majalisar dattawa da gwamnan jiharsa.

A cewar tsohon gwamnan, gaba daya shugabannin PDP sun ce masa "ka karbi mukamin"; saboda haka, ya bukaci yan Najeriya da su share yan bakin ciki da ke neman a dakatar da shi daga PDP.

Ga bidiyon a kasa:

“Zan yi aiki kamar magini”, sabon ministan ilimi

A wani labarin, mun ji cewa sabon ministan ilimi a gwamnatin Bola Tinubu, Farfesa Tahir Mamman, ya shiga ofis domin fara aiki kan muƙamin da Tinubu ya ba shi.

Mamman na cikin ministoci 45 da Shugaba Bola Tinubu ya rantsar a ranar Litinin, 21 ga watan Agustan 2023 a fadar shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng