Najeriya Ta Samu Shiga Jerin Kasashen Nahiyar Afirka 10 Mafi Karfin Masana'antu
- A wata sabuwar sanarwa da aka fitar, Najeriya ta samu zarafin kasancewa daga cikin kasashe 10 mafi karfin masana'antu a Nahiyar Afirka
- Rahoton wanda Bankin Raya Nahiyar Afirka (AfDB) da ya fitar tare da hadin gwiwar hukumar ci gaban masana'antu a Nahiyar
- Wannan rahoto ya yi duba zuwa ga ci gaban masana'antu da ake samu a kasashen daban-daban a Nahiyar ta fannoni da dama
FCT, Abuja - Najeriya ta samu shiga jerin kasashen Nahiyar Afirka 10 da su ka fi karfin masana'antu.
Wannan na zuwa ne bayan kasar da ke Yammacin Nahiyar Afirka ta rasa gurbi a jerin kasashe mafi tattalin arziki 10 a Nahiyar, kamar yadda Bankin Duniya ta tattaro.
Meye rahoton ya ce kan Najeriya?
Rahoton wanda Bankin Raya Afirka (AfDB) ta hadin gwiwar Kungiyar Tarayyar Afrika (AU) da kuma Cibiyar Masana'antu ta Afrika su ka wallafa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoton ya yi duba zuwa ga ci gaban masana'antu na kasashen da inganta fitar da kayayyaki sai kuma fadada hanyoyin samun kudade.
Rahoton ya kunshi kasashe 52 ba tare da Somalia da Sudan ta Kudu ba saboda rashin isasshen bayanai akansu.
Jerin kasashen Nahiyar Afirka 10 da Legit.ng ta lissafo wadanda su ka fi karfin masana'antu.
1. Afirka ta Kudu
2. Morocco
3. Masar
4. Tunisia
5. Mauritius
6. Eswatini
7. Senegal
8. Najeriya
9. Kenya
10. Namibia
A bangaren ci gaban masana'antu, Nahiyar Afirka ta Arewa ita ce kan gaba fiye da ko ina.
Yanki mai biye mata ita ce Kudancin Afirka sai Afirka ta Tsakiya sai Afirka ta Yamma sannan Afirka ta Gabas.
Najeriya Ta Rasa Matakin Farko A Masu Fitar Da Mai A Afirka
A wani labarin, Najeriya ta rasa matakin farko a jerin kasashen Afirka da su ka fi samar da man fetur a Nahiyar.
Kasar a baya ita ce kan gaba a kasashe da su ka fi samar da mai a Nahiyar kafin Libya ta sha mata kai inda Najeriya ta koma mataki na uku a jerin kasashen.
Wannan na zuwa ne bayan kasar ta rasa matsayinta har ila yau, a cikin kasashe mafi tattalin arziki a Nahiyar.
Asali: Legit.ng