Ana Shirin Nada Sababbin Ministoci, El-Rufai Ya Dankaro Shagube a Shafin Twitter
- Yau za a nada sababbin Ministocin Najeriya, Nasir El-Rufai ya yi maganar farko a shafin Twitter
- Tsohon Gwamnan Kaduna ya dawo shafin da karfinsa, ya tsakuro wata tsohuwar wakar Bob Marley
- Kusan dai za a iya cewa El-Rufai ya na shagube ne ga duk wanda ya tsargu bayan abin da ya faru
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Dublin - A karon farko a cikin makonni uku, Nasir El-Rufai, ya tuna da shafinsa na X wanda mutane su ka fi sani da Twitter.
Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana a dandalin sada zumuntan a ranar Lahadi, ya saki kalamai masu harshen damo.
Malam Nasir El-Rufai wanda aka ki tantacewa ya zama minista ya tuna da wata waka da Bob Marley ya rera a lokacin rayuwarsa.
El-Rufai ya dauko wakar shekara 47
A daidai lokacin da za a rantsar da sababbin ministoci a yau, sai aka ji ‘dan siyasar ya dauko wannan waka ta ‘Who The Cap Fit’.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wakar fitaccen mawakin wanda ya rayu tsakanin 1966 da 1981 a Jamaika, za a ji yadda ya ke bayanin rashin adalcin ‘dan adam.
"Mutum da mutum babu adalci, yara/Ba ka san wa za ka yarda da shi ba/Babban makiyinka zai iya zama babban abokinka/
Kuma babban abokinka, ya zama babban makiyi/Wasu za su ci kuma su sha tare da kai."
- Bob Marley
Malam El-Rufai ya dawo Twitter
Wannan waka da aka rera da Ingilishi a 1976 ta yi magana a kan munafukai, ta na mai nuna cewa duk wanda ya tsargu, da shi ake magana.
Kafin nan Nasir El-Rufai ya dauko wani gajeren labarin abin da ya faru tsakanin Deng Xiaoping da jikinsa, Mao Zedong a wajen Chairman Mao.
An kawo labarin tsohon shugaban na Sin ne domin tallata tsarin jari hujja kan manufar gurguzu. Kafin nan Malam ya yabi gwamnatin Tinubu.
Kafin a je ko ina aka ji Sanata Shehu Sani a shafinsa ya na wani abin mai kamar martani, ya na cewa:
"Na maida shi ya zama mawakin Reggae da Rastafarian.’
Kwankwaso da Atiku sun hadu
Ku na da labari Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi bakuncin tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar a gidansa da ke garin Abuja.
Yayin da Abdullahi Ganduje ya hadu da Nyesom Wike, Atiku ya hadu da madugun Kwankwasiyya, hakan ya bar masu nazarin siyasa da dogon tunani.
Asali: Legit.ng