Juyin Mulki: Dakta Gumi Ya Ce Wurin Tinubu Ya Kamata Malamai Da Sarakuna Su Fara Zuwa Ba Nijar Ba
- Sheikh Dakta Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya yi magana kan juyin mulkin jamhuriyar Nijar
- Ya ce fadar shugaban Najeriya ya kamata malamai da sarakunan da suka je Nijar ya kamata su je
- Ya kuma ce kamata ya yi Gwamnatin Najeriya ta mayarwa da jamhuriyar Nijar wutar lantarkinta da aka datse
Kaduna - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dakta Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya tofa albarkacin bakinsa dangane da ziyarar da malamai, sarakuna da wakilan ECOWAS suka kai Nijar.
Ya ce fadar shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kamata su je domin neman sulhu ba jamhuriyar Nijar ba.
Dakta Gumi ya bayyana hakan ne a wani ɗan taƙaitaccen bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi, 20 ga watan Agustan da muke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Gumi ya ce wajen Tinubu ya kamata su je ba Nijar ba
Sheikh Ahmad Gumi ya ce ba Nijar ya kamata Abdulsalami da sarkin Musulmi su je ba, fadar Shugaba Tinubu ya kamata su je domin su faɗa ma sa abinda ya kamata ya yi.
Ya ce datse wutar lantarkin da Najeriya ke bai wa Nijar da aka yi, dai dai yake da fara yaƙi da ƙasar da ake ƙoƙarin ganin an yi sulhu da ita.
Ya ƙara da cewa bai kamata manyan Najeriya su bari Turawan Yamma su zugasu wajen shiga sha'anin siyasar wata ƙasa ba.
Dakta Gumi ya nemi malamai su ba Tinubu shawara
Sheikh Dakta Gumi ya kuma ce kamata ya yi malaman da Shugaba Bola Tinubu ya tura Nijar sulhu su faɗa ma sa cewa ya maidawa jamhuriyar Nijar wutar lantarkin da aka datse, sannan kuma a bude kan iyakokin ƙasashen biyu.
Shugaban mulkin sojin Nijar, Abdourahmane Tchiani ma ya yi kira ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta yi ƙoƙarin mayarwa da ƙasar wutar lantarkin da aka datse.
Ya ce takunkumin wutar lantarkin na wahalar da 'yan Najeriya da dama, musamman ma majinyata da ke kwance a asibitocin ƙasar a halin da ake ciki.
Tchiani ya ce za su kare Nijar daga hare-haren ECOWAS
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan martanin da shugaban juyin mulkin jamhuriyar Nijar, Abdourahmane Tchiani ya yi wa kungiyar ECOWAS.
Ya ce a shirye suke su kare jamhuriyar Nijar daga dukkan wasu hare-hare duk da dai ba son yaƙin suke yi ba.
Asali: Legit.ng