Akwai Yiwuwar Tinubu Ya Bi Tafarkin Tsohon Shugaba Buhari, Zai Iya Rike Mukamin Ministan Man Fetur
- Mai yiwuwa shugaba Bola Tinubu ya nada kansa a matsayin ministan albarkatun man fetur da kuma sabuwar ma’aikatar albarkatun iskar gas da aka kafa
- Duk da cewa bai fito karara ya tabbatar da hakan ba, rashin nada wasu daga cikin ministocinsa a wadannan mukamai na nuna sha'awarsa ga hakan
- Ya nada tsohon Sanata Heineken Lokpobiri a matsayin karamin minista a ma’aikatar man fetur, sannan kuma ya nada Ekperikpe Epko a matsayin karamin ministan albarkatun iskar gas
Fadar shugaban kasa, Abuja – Mai yiwuwa shugaban kasa Bola Tinubu ya bi sahun magabacinsa Muhammadu Buhari wajen nada kansa a matsayin ministan albarkatun man fetur da sabuwar ma’aikatar albarkatun iskar gas.
Tinubu, a ranar Laraba, 16 ga watan Agusta, ya baiwa ministocinsa mukamai tare da bayyana inda za su yi a gwamnatinsa.
Sai dai, shugaban kasar bai nada wasu ministoci ba domin jagorantar ma'aikatun iskar gas da albarkatun man fetur ba.
A dai jira tukuna
Ko da yake bai bayyana kai tsaye cewa yana da niyyar rike mukamin ministan man fetur ba, rashin nada wani a wannan mukamin na nuni da cewa shugaba Tinubu na neman rike mukamin ne, inji Premium Times.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar ta kara da cewa mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya ki cewa komai game da wannan lamari.
Ya zuwa yanzu, akwai kananan ministoci a ma'aikatun, amma babu mai rike da kujerar babban minista.
Lokpobiri ya zama shugaban ma'aikatar man fetur a matsayin karamin minista
A halin da ake ciki kuma, Heineken Lokpobiri, tsohon dan majalisar dattawan Najeriya, ya samu kujerar karamin ministan man fetur.
Hakazalika, Emperikpe Epko, wanda tsohon dan majalisar wakilai ne, an nada shi a matsayin karamin ministan albarkatun iskar gas.
Tun farkon mulkin Buhari zuwa karshe, shi ke rike da ma’aikatar albarkatun man fetur a Najeriya, kuma hakan bai kawo wani sauyi ba a yanayin wadatuwa da saukin mai a kasar.
Ministoci 5 da za su kula da tsaro
A wani labarin, babu bangaren da 'yan Najeriya su ka fi bukatar sauyi cikin gaggawa kamar harkar tsaro, ganin yadda bangaren ke lakume makudan kudade a kasar musamman lokacin kasafin kudi na karshen shekara.
Rashin tsaro ta dawo babbar barazana ga kasancewar Najeriya inda ya mamaye kasar baki daya daga Arewaci har zuwa Kudanci.
A kokarin dakile matsalar tsaro, Shugaba Bola Tinubu ya daura nauyin kawo karshen rashin tsaron ga ministoci biyar.
Asali: Legit.ng