Yan Sanda Sun Kama Karin Mutum 3 Cikin Wadanda Suka Yi Wa Sarkin Kano Ihun ‘Sabon Gwamna Sabon Sarki’

Yan Sanda Sun Kama Karin Mutum 3 Cikin Wadanda Suka Yi Wa Sarkin Kano Ihun ‘Sabon Gwamna Sabon Sarki’

  • Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama Abdulrazak Usman Sarki, Fatihu Muktar Faruk da Usman Baba Attah
  • Ana zargin matasan uku suna cikin jerin matasan da suka yi wa Sarkin Kano, Alhaji Aminu Adeo Bayero rashin kunya a wajen wani taro
  • Tun da farko an kama wasu daga cikin wadanda suka yi wa Sarkin ihun 'Sabon Gwamna Sabon Sarki' a kusa da fada

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama masu matsakaicin shekaru su uku cikin wadanda ake zargi da zanga-zanga a kan Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a wajen wani taro da aka yi kwanan nan a kusa da fadar sarkin.

Wadanda aka kama sun hada da Abdulrazak Usman Sarki, Fatihu Muktar Faruk da Usman Baba Attah, rahoton The Guardian.

Yan sanda sun sace cafke wasu cikin wadanda suka yi wa sarkin Kano ihu
Yan Sanda Sun Kama Karin Mutum 3 Cikin Wadanda Suka Yi Wa Sarkin Kano Ihun ‘Sabon Gwamna Sabon Sarki’ Hoto: @HrhBayero
Asali: Twitter

Ko da yake, yan sanda sun gano wasu mutane shida da aka kama tun da farko da taimakon faifan bidiyo da aka tura a wurin da aka gudanar da zanga-zangar, jaridar Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Neman Alawus: Bidiyon Tubabbun Yan Boko Haram Suna Zanga-Zanga a Borno, Sun Rufe Hanya

Za mu kamo sauran da masu daure masu gindi, yan sanda

Sai dai kuma, rundunar ta yi nuni da cewar an fara wani farauta cike da dabaru don bankado sauran mutanen da kuma masu daukar nauyinsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kwamishinan yan sandan jihar, CP Mohammad Usaini Gumel ya tabbatar zanga-zangar rashin da'ar a lokacin kaddamar da asibitin Hasiya Bayero, kusa da fadar sarkin inda wasu mutane suka mamaye wajen suna ihun 'Sabon Gwamna, Sabon Sarki'.

A cewar shugaban yan sandar, mummunan al'amarin ya faru ne a gaban Gwamna Abba Kabir Yusuf da shi kansa sarkin lokacin da mutanen bayan mamaye wajen, inda suka rika yada kalamai masu tayar da hankali.

Wannan al'amari ya haifar da rashin tsaro a masarautar musamman a bangaren mai martaba. Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran manyan baki da aka gayyata.

Kara karanta wannan

Cin Hanci: Abba Gida Gida Ya Tsorata, Ya Bukaci Binciken Gaggawa A Kotun Sauraran Korafe-Korafen Zabe

Kwamishinan yan sandan jihar ya ce:

"Da samun rahoton wannan wannan abun kunyar, ni kwamishinan yan sandan jihar Kano, na aika da runduna ta musamman domin gano tare da cafke wadanda suka aikata wannan abu tare da masu daukar nauyinsu.
"Bincike da aka yi ta hanyar amfani da fasahar zamani ya yi sanadiyar kama mutum uku. sune Abdulrazak Usman Sarki, mai shekaru 36 na Disu Quarters, karamar hukumar Gwale, Fatihu Muktar Faruk,mai shekaru 35 na fadar sarkin Kano da Usman Baba Attah, mai shekaru 25 na Kabara Quarters, karamar hukumar Kano Municipal. A halin da ake ciki, ana ci gaba da gudanar da bincike na musamman da nufin kamo sauran wadanda ke da hannu a ciki."

Yan sanda ba za su lamunci muzanta masarautar Kano ba

A wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa ya saki, kwamishinan yan sandan ya yi gargadin cewa ba za su lamunci yunkurin wani mutum na muzanta masarautar Kano ba duk matsayinsa.

Kara karanta wannan

Yaran El-Rufai Sun Lallaba Sun Roki Shugaban Kasa ya Ba Shi Kujerar Minista

Ya dage cewa za su nuna turjiya ga duk wani yunkuri na daukar nauyin wasu don yin ba'a ga sarkin.

Bugu da kari, rundunar ‘yan sandan ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an samar da tsaro, kariya, zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al’ummar jihar.

Matashi ya yi tattaki daga Bauchi zuwa Kano don ganin Aisha Humaira

A wani labari na daban, mun ji cewa wani matashi mai suna Adamu ya yi tattaki daga jihar Bauchi zuwa jihar Kano domin ya yi ido hudu da shaharriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Aisha Humaira.

Sai dai kuma, matashin ya hadu da sharrin barayi inda suka karbe masa komai a nan jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng