Yadda Matasa Suka Babbaka Wani Mai Satar Yara a Arewacin Najeriya, Sun Ceto Mata 2 Da Ya Sace
- Fusatattun matasa sun kama tare da babbaka wani mai satan yara a karamar hukumar Lapai ta jihar Neja
- Mutumin ya dade ya sace yara musamman yan makaranta a ciki garin Lapai da kewaye kafin dubunsa ta cika
- Wani mazaunin garin Lapai ya tabbatarwa Legit.ng da faruwar al'amarin
Jihar Niger - Fusatattun matasa sun babbaka wani da ake zaton dan asiri ne a garin Lapai, hedkwatar karamar hukumar Lapai ta jihar Neja.
Lamarin ya afku ne a ranar Juma'a, 18 ga watan Agusta, jim kadan bayan idar da Sallar Juma'a, jadriar Vanguard ta rahoto.
An kama mai satar yara a Lapai
Kafin a kona shi, wanda ake zargin mai suna Dule Sakon Kano wanda ke tsare da yara biyu, ya fallasa cewa ya dade yana aikata ta'asar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya tona cewa yana kai yaran makaranta da yake sacewa ga ubangidansu a yankin.
An shafe tsawon watanni ana ta fama da sace-sacen yara kanana a ciki da wajen garin Lapai.
An kama wanda ake zargin tare da yara biyu, wadanda shekarunsu bai gaza tsakanin hudu da biyar ba, inda ya shirya kai su wani wuri da ba a sani ba lokacin da dubunsa ya cika.
An tattaro cewa an tura yaran biyu ne domin su siyo wasu kayan amfani gida a wani shago da ke kusa da su da misalin karfe 1:30 na ranar Juma'a jim kadan kafin a fara Sallah.
Wani da abun ya faru a kan idonsa ya ce:
"Wanda ake zargin, kafin a kona shi, ya yarda cewa ya aikata laifin kuma cewa yana a hanyarsa na kai su wajen ubangidansa.
"Fusatattun matasan sun dauki doka a hannunsu biyo bayan yawan batan yara daga yankin a yan baya-bayan nan ba tare da jami'an tsaro sun kama kowa ba.
"Wanda ake zargin ya ci na kare lokacin da mutane suka gano abun da yake son aikatawa sannan suka kama shi a hanyar makarantar sakandare na mata, hanyar makabarta sannan suka ja shi a titi har zuwa tsakiyar garin Lapai inda suka kona shi kurmusa."
Fusatattun matasan sun kona shi kafin isowar yan sanda
Ya ce kafin jami'an yan sandan Lapai su isa wajen da abun ya faru, an riga an kona wanda ake zargin ta yadda ba ma za a iya gane shi ba kuma matasan sun bace daga wajen.
Legit.ng ta tuntubi wani mazaunin garin Lapai wanda ya nemi a sakaya sunansa inda ya tabbatar da faruwar al'amarin.
Ya ce:
"Eh da gaske ne, an dan dauki lokaci yanzu ana sace yara musamman yan makaranta ba tare da an san wanda ke aikata haka ba. Allah dai ya toni asirinsa aka kama shi. Kuma da gaske ne an kona shi kurmus. Muna kuma rokon Allah ya tona asirin sauran abokan harkarsa don ya tabbatar da ba shi kadai bane suna da ubangida."
An girke matakan tsaro a jihar Neja, mutane na dar-dar
A wani labarin, mun ji cewa bayan tagwayen hare-hare da yan bindiga suka kai jihar Neja a daren Lahadi da safiyar Litinin wanda ya yi sanadiyar rasa rayukan sojoji 36, mazauna jihar ta arewa maso tsakiya sun cika da fargaba, jaridar Punch ta rahoto.
An samu karin motocin sojoji da na sauran jami'an tsaro a wurare da dama a babban birnin jihar. An kuma gano manyan motoci cike da sojoji suna tunkarar hanyar Shiroro, karamar hukumar da aka kai hare-haren.
Asali: Legit.ng