Ministoci: Na Hannun Daman Atiku Ya Ambaci Kuskure Bayan Tinubu Ya Rabawa Ministoci Ma'aikatu
- Jigo a jami'iyyar PDP, Barista Daniel Bwala ya soki rarraba ma'aikatu na ministocin Tinubu
- Bwala ya kasance na hannun daman dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar
- Ya ce ta yaya za a dauki ma'aikatar tsaro a ba wa Bello Matawalle da ya gagara kawo karshen rashin tsaro a jihar Zamfara
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Barista Daniel Bwacha na hannun daman dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ya magantu kan ministocin Shugaba Tinubu.
A ranar Laraba 16 ga watan Agusta, Tinubu ya ba wa sabbin ministoci ma'aikatu wadanda majalisar Dattawa ta tantance, Legit.ng ta tattaro.
Meye Bwala ya ce kan mukaman ministoci?
Barista Bwala ya ce a mukaman akwai wadanda ba su dace da ma'aikatun da aka ba su ba ko kadan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce dukkan ministocin ba su da alaka kuma ba su dace da mukamin ba ganin yadda Tinubu ya rarraba su.
Ya ce:
"Akwai ministoci kwararru amma ma'aikatun da aka ba su ba su dace da su ba."
Bwala ya ba da misalin Hannatu Musawa da aka ba wa ministar al'adu madadin ma'aikatar jin kai, Vanguard ta ruwaito.
Shin Matawalle ya dace da ministan tsaro?
Hannatu ta fito daga jihar Katsina da ke yankin da ya ke bukatar jin kai ga mutane saboda matsalolin tsaro.
Jigon PDP ya kuma koka kan yadda Bola Tinubu ya damkawa Bello Matawalle karamin ministan tsaro.
Bwala ya ce ta yaya mutumin da ya gagara dakile matsalar tsaro a jihar Zamfara zai yi kokari a tsaron kasa baki daya.
Ya ce ma'aikatar tsaro na taka muhimmiyar rawa wurin tabbatar da kare kasa daga hare-hare da kuma zaman lafiyar al'umma.
Tinubu Ya Raba Mukaman Ministoci
A wani labarin, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da ma'aikatun ministoci 45 da aka kammala tantancewa a majalisar Dattawa a kwanakin baya.
Daga cikin ministoci 48, an tabbatar da 45 yayin da guda uku ke jiran sakamakon bincike da ake yi a kansu.
Daga cikin wadanda su ka samu mukaman akwai Nyesom Wike, ministan Abuja sai Badaru Abubakar, ministan tsaro da kuma Bello Matawalle karamin ministan tsaro.
Asali: Legit.ng