Tsadar Rayuwa Ta Sa Magidanta Satar Amfanin Gona A Jihar Taraba
- Wahala ta sa magidanta na satar kayayyakin gona don ciyar da iyalansu a jihar Taraba
- Manoma da dama a kwanakin nan sun sha kama magidanta na dibar amfanin gona don ci da iyalansu
- Wata mai gona, Lami John ta ce ta kama makwabcinta na dibar rogo a gonarta don kai wa gida a ci
Jihar Taraba - Ana zargin magidanta da satar kayayyakin gona a jihar Taraba don ciyar da iyalansu saboda halin da ake ciki.
Daga cikin kayayyakin da ake yawan sata a gona akwai rogo da masara da doya wanda hakan bai rasa nasaba da irin halin kunci da ake ciki.
Me yasa magidantan satar kayan gona?
Rahotanni sun bayyana cewa satar ta yi kamari a kwanakin nan yayin da tsadar rayuwa ta yi wa mutane katutu.
"Fastoci Na Kwanciya Da Ita": Dan Shekara 84 Ya Kashe Matarsa Yar Shekara 75 Kan Rashin Bashi Hakkin Kwanciyar Aure
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wata mata mai gona a wani kauyen Taraba ta ce ta kama wani makwabcinta ya na dibar rogo a gonar don kai wa iyalansa, RFI ta tattaro.
Matar mai suna Lami John ta ce ba ta kai shi kara ko ina ba musamman da ya ce shi ya debi rogon ne don su ci a gida ba wai ya siyar ba.
Ta ce:
"Da naji haka sai na ce masa ya tafi kawai ba tare da na kai kararsa wurin mai unguwa ba, saboda na san shi mutumin kirki ne."
Meye manoman ke cewa kan satar kayan gona?
Wani mai gona, Ibrahim Sulaiman ya ce ta sha kama magidanta a gonarsa na satar kaya amma bai taba kai su kara ba saboda ya san halin da ake ciki.
Tun bayan cire tallafin mai da Shugaba Bola Tinubu ya yi kayayyaki su ka yi tashin gwauron zabi, cewar Daily Trust.
Rikita-rikita Yayin Da Mata Ta Fashe Da Kuka Bayan Mai Tura Baro Ya Tsere Mata Da Kaya, An Ba Ta Taimako
Ko a jiya ma wasu matan aure sun yi zanga-zanga a Rigasa da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Matan sun yi zanga-zangar ne don nuna damuwa da irin halin da ake ciki na tsadar abinci.
Matasa Sun Fasa Rumbun Abinci A Taraba
A wani labarin, wasu matasa sun fasa babban rumbun ajiyar abinci a jihar Taraba don dibar ganima.
Rahotanni sun tabbatar cewa rumbun abincin na wani dan majalisa ne kuma tsohon shugaban karamar hukumar Sardauna da ke jihar.
Asali: Legit.ng