Tinubu vs Atiku, Obi: An Gargadi Kotun Zabe Kada Ta Yi Hukuncin Da Zai Tayar Da Rikici
- Wata ƙungiya ta gargaɗi kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa da kada ta yi wani hukunci da zai kawo rikici a ƙasar nan
- An buƙaci kotun da ta tabbatar ta yi gaskiya da adalci a hukuncinta kan ƙalubalantar nasarar Tinubu da ake yi a gabanta
- Ƙungiyar ta bayyana cewa ido ya koma kan ɓangaren shari'ar sannan duk wani hukuncin da bai yi wa ƴan Najeriya daɗi ba zai iya haifar da rikici
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - An gargaɗi kotun sauraron ƙarrakin zaɓen shugaban ƙasa da kada ta yi hukuncin da zai kawo rikici a ƙasar nan.
Kakakin ƙungiyar Diaspora Action for Democracy in Africa (DADA), Great Jonathan, shi ne ya yi gargaɗin a wajen taron ganawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis, 17 ga watan Agustan 2023, cewar rahoton The Cable.
Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC Ta Zargi Gwamnatin Kano Da Ba Alkalai Cin Hancin N10m, Ta Bayar Da Dalilai
Jonathan ya bayyana cewa ido ya koma kan ɓangaren shari'a saboda tana da ƙarfin da za ta iya kawar da barazanar ɓarkewar rikicin da ƙasar nan ke fuskanta.
An gargaɗi kotu kan shari'ar shugaban ƙasa
Ya ƙara da cewa masu kaɗa ƙuri'a sun san wanda suka zaɓa fiye da kotun sannan suna jiran kotun ne kawai saboda suna mutunta doka da oda.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa:
"Amma tun da haƙƙin kotu ne tabbatar da gaskiya da adalci duk lokacin da aka kawo ƙara a gabanta, domin zaman lafiya da ƙwanciyar hankali, an ba kotu cikakkun hujjoji domin gano haƙiƙanin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023."
"Dangane da tattaunawar da mu ka yi da ƴan Najeriya da dama, sun nuna damuwarsu kan cewa ɓangaren shari'a yakamata ya lura sosai saboda idan hukuncin kotun bai gamsar ba, zai iya fusata matasa su tayar da rikici a ƙasa."
Gwara Haka: Yadda Rikicin Kabilanci a Tsakanin Mayakan Boko Haram Ya Salwantar Da Rayukan Mayaka Kusan 100
An Bayyana Yan Hana Ruwa Gudu a Gwamnatin Tinubu
A wani labarin na daban kuma, babban faston cocin INRI Evangelical Spiritual Church, ya yi hasashen ƴan hana ruwa gudu a gwamnatin Shugaba Tinubu.
Primate Elijah Ayodele ya bayyana cewa ƴan hana ruwa gudun sun fito ne daga yankin Kudu maso Yamma na ƙasar nan.
Asali: Legit.ng