Binciken Emefiele da CBN Ya Jawo Jami’an DSS Sun Cafke Shugaban NIRSAL
- Abbas Umar Masanawa ya samu kan shi a hannun hukumar DSS masu fararen kaya a Najeriya
- Ana ganin kama kwararren ma’aikacin bankin bai rasa nasaba da alakarsa da Godwin Emefiele
- Tsohon Gwamnan wanda yanzu ya na hannu, ya yi sanadiyyar zaman Masanawa shugaban NIRSAL
Abuja - Hukumar DSS masu fararen kaya sun cafke shugaban hukumar NIRSAL mai harkar bada bashin aikin gona, Abbas Umar Masanawa.
Zuwa yanzu ba a tabbatar da dalilin kama Abbas Umar Masanawa ba, majiyoyin Daily Trust ta ce bai rasa nasaba da alaka da Godwin Emefiele.
Abbas Masanawa ya jagoranci hukumar NSPMC da ke da alhakin buga kudi a Najeriya.
An damke Gwamnan CBN
Tun da Bola Ahmed Tinubu ya dare mulki a karshen Mayun 2023, aka fara binciken ayyukan da su ka faru a bankin CBN a lokacin Mista Emefiele.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Daf da zaben 2023, Masanawa ya ajiye mukamin da yake kai, ya nemi takarar Gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.
Ma’aikacin bankin ya gwabza da Dikko Radda, Mustapha Inuwa, Ahmad Dangiwa da sauransu a zaben fitar da gwani kafin Radda ya samu tikitin.
A yayin da ya ke darekta mai kula da tattalin arziki da dabaru a NSPMC, Godwin Emefiele ya bada shawarar nada shi ya zama shugaban kamfanin.
Sahara Reporters ta fitar da rahoton cafke jami’in, amma har yanzu DSS ba ta yi karin haske a kan dalili da zargin da ke kan wuyan Masanawa ba.
Da aka tuntubi Peter Afunanya domin jin ta bakinsa, bai amsa sakonnin ‘yan jarida ba.
NSPMC, NIRSAL zuwa DSS
Kafin yanzu, an zargi Aliyu Abdulhameed da badakalar naira biliyan 5 a lokacin da yake ofis, shi ya rike hukumar gwamnatin tarayyar kafin zuwan Masanawa.
Awon gaba da kudin manoman Jigawa da Kano ya yi sanadiyyar da Mai girma Muhammadu Buhari ya fatattaki Abdulhameed a Disamban 2022.
Bayan ya ajiye mukaminsa ya yi takarar gwamna a gida, kafin ya bar ofis a karshen watan Mayu, sai shugaban Najeriya Buhari ya ba shi rikon NIRSAL.
Siyasar APC bayan zaben 2023
An samu labari Abdullahi Umar Ganduje ya na cigaba da karbar ‘ya ‘yan jam’iyya a sakatariyar APC bayan da ya maye gurbin Abdullahi Adamu a NWC.
Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Hon. Benjamin Kalu ya kai wa jagoran na sa ziyara ya ce kyau Bola Ahmad Tinubu ya karawa Ibo ministoci.
Asali: Legit.ng