Najeriya Ta Yi Asarar Dala Biliyan 46 Na Danyen Mai Saboda Satar Man Da Ake

Najeriya Ta Yi Asarar Dala Biliyan 46 Na Danyen Mai Saboda Satar Man Da Ake

  • A rahoton kwanan nan an tabbatar cewa Najeriya ta yi asarar Dala biliyan 46.16 saboda satar danyen mai
  • Hakan ya faru ne saboda yawan satsace-sacen da ake samu na danyen mai daga 2009 zuwa 2020
  • Wannan na zuwa ne bayan kamfanin NNPC ya ce an samu satar mai din sau 114 a mako daya

FCT, Abuja - Kamfanin mai na NNPC ya ce ya yi asarar fiye da Dala biliyan 46 na gangan danyen mai miliyan 612 a cikin shekaru 10.

NNPC ya ce yawan satar mai da ake a kasar ya wuce hankali wanda hakan ke jawo wa kamfanin da Najeriya asara ta makudan kudade, Legit.ng ta tattaro.

Najeriya ta yi asarar Dala biliyan 46 kan satar danyen mai a kasar
An Samu Satar Danyen Mai Din Har Sau 114 A Cikin Mako Daya. Hoto: Anadolu Agency / Contributor.
Asali: Getty Images

Wane irin asara Najeriya ta yi?

Hukumar Hakar Ma'adinai ta Najeriya (NEITI) ita ta tabbatar da haka a wani rahoto da ta fitar yayin wata ganawa ta musamman.

Kara karanta wannan

DSS: ‘Yan Ta’adda Sun Yi Shirin Kai wa Mutane Mugun Hari a Jirgin Abuja-Kaduna

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

NEITI ta ce tsakanin 2009 zuwa 2020, Najeriya ta yi asarar gangan mai 140,000 a rana saboda satar danyen mai wanda kudin ya kai Dala miliyan 10.7 a rana.

Rahoton ya lissafo yawan kudin da kamfanonin Gas da Mai da kuma ma'adinai ke ba wa Najeriya da kuma yawan kudin da kasar ke karba.

Najeriya a makwanni masu zuwa za ta yi hadaka da wasu masu ruwa da tsari don zuba hannun jari ta yadda za a samu bunkasar wadatuwar mai a kasar.

Kasar na fatan inganta fitar da man zuwa ganga miliyan 1.7 a rana zuwa watan Nuwamba.

Yawan satar danyen mai a Najeriya

Najeriya za ta tabbatar da hakan ne don cike umarnin da Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Mai (OPEC) ta gindaya.

Saboda matsalolin satar man da kuma fasa bututun mai, Najeriya ta gaza cike umarnin OPEC na samar da mai din a duniya.

Kara karanta wannan

Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati

Wannan na zuwa baya kamfanin NNPC ya sanar da cewa ya samu rahoton satar mai har sau 114 daga ranar 4 zuwa 11 ga watan Agusta.

Jihohin da aka fi satar mai din a Najeriya sun hada da Bayelsa da Imo da Delta da kuma Rivers.

Najeriya Ta Rasa Matakin Farko Na Fitar Mai A Afirka

A wani labarin, Najeriya ta rasa matakin ta na farko a jerin kasashe masu fitar da man fetur a Nahiyar Afirika.

Kasar Libya yanzu ita ke kan gaba bayan doke Najeriya da ke matakin farko a kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.