Kwamandan Boko Haram Da Ya Jagoranci Rikicin Kabilancin Da Ya Yi Sanadin Halaka Mayaka 82 Ya Mika Wuya

Kwamandan Boko Haram Da Ya Jagoranci Rikicin Kabilancin Da Ya Yi Sanadin Halaka Mayaka 82 Ya Mika Wuya

  • Babban kwamandan Boko Haram Amir Bukkwaram da ya jagoranci rikicin ƙabilanci ya miƙa wuya
  • Bukkwaram shi ne ya haddasa rikici tsakanin ƙabilun Fulani, Hausa, Kanuri da Baduma da ke cikin kungiyar ta Boko Haram
  • Ya miƙa wuya ne ga jami'an haɗin gwiwa na ƙasa da ƙasa tare da iyalansa da wasu daga cikin yaransa

Borno - Kwamandan Boko Haram da ya haddasa rikicin ƙabilanci tsakanin 'yan ta'adda wanda ya kai ga kashe mayaka 82 ya mika wuya ga sojoji.

An bayyana cewa kwamandan mai suna Amir Bukkwaram, ya miƙa wuya tare da iyalansa, mayaƙan da ke tare da shi, tarin dabbobi da kuma makamai ga sojoji.

Kwamandan Boko Haram Amir Bukkwaram ya miƙa wuya
Kwamandan Boko Haram da ya jagoranci kashe mayaƙa 82 ya miƙa wuya ga jami'an tsaro. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Babban kwamandan Boko Haram ya miƙa wuya

Daily Trust ta ruwaito cewa Amir Bukkwaram na daga cikin waɗanda suka yi fice a cikin mayaƙan na Boko Haram da ke gaɓar Tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Na Shirin Tattaunawa Da 'Yan Bindiga, Ya Bayyana Dalilansa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An bayyana cewa Bukkwaram na daga cikin 'yan ta'addan da suka yi wa yankin na Tafkin Chadi farin sani fiye da sauran mayaƙan na Boko Haram.

An ɗauki Bukkwaram da mutanen da suka miƙa wuya a tare, da makamai da kuma dabbobinsu, zuwa sashe na uku na rundunar haɗin gwiwa na ƙasa da ƙasa da ke Mongunu.

Yadda mayaƙan Boko Haram 82 suka mutu a rikicin ƙabilanci

A baya Legit.ng ta kawo rahoto kan yadda mayaƙan Boko Haram aƙalla 82 suka sheƙa barzahu a wani rikici na ƙabilanci da ya ɓarke a tsakaninsu.

Lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Kukawa da ke jihar Borno, inda aka gwabza yaƙi tsakanin ƙabilun Fulani, Hausa, Kanuri da kuma Buduma da ke cikin kungiyar ta Boko Haram.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jami'an sojojin Najeriya ke ci gaba da ragargazar 'yan ta'addan ma Boko Haram a cikin kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Gwara Haka: Yadda Rikicin Kabilanci a Tsakanin Mayakan Boko Haram Ya Salwantar Da Rayukan Mayaka Kusan 100

'Yan Boko Haram sun cafke mayaƙan ISWAP 60

Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan mayaƙan ISWAP aƙalla 60 da 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram suka kama a wani samame da suka kai mu su.

An bayyana cewa mayaƙan Boko Haram, suna yawan samun nasara akan mayaƙan ISWAP a rikice-rikecen da ke wakana tsakaninsu cikin kwanakin nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng