Ba Kyauta Ba Ne: An Gano Ashe Naira Biliyan 5 da Za a Raba Wa Jihohi Bashi Ne

Ba Kyauta Ba Ne: An Gano Ashe Naira Biliyan 5 da Za a Raba Wa Jihohi Bashi Ne

  • Sai daga baya aka lura kdin tallafin da za a rabawa Jihohi bashi ne ba kyautar Gwamnatin Tarayya ba
  • Janye tsarin biyan tallafin fetur ya jawo Bola Ahmed Tinubu zai taimakawa Jihohin da su ke da sha’awa
  • Daga baya kowace Jiha za ta dawo da kudin aka ba ta, sai dai bashin bai kunshe da ribar da aka saba ci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Tallafin da gwamnatin tarayya ta fito da shi domin rabawa gwamnonin jihohi sakamakon cire tallafin man fetur da aka yi, ba kyauta ba ne.

Akasin yadda aka yi tunani da farko, The Cable ta fitar da rahoto na musamman cewa wannan tallafi bashi ne ba kyautar da ake tunani ba.

Da yake jawabi bayan taron NEC, Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum ya fadi jerin tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta fito masu da su.

Kara karanta wannan

Kungiyar NLC Ta Ki Amincewa Da Shirin Ba Wa Gwamnoni N5bn Na Tallafi, Ta Fadi Dalilai

tinubu da gwamnoni
Tinubu ya ba Gwamnonin Jihohi bashi Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Wasikar DG NGF ta fito

A wata wasika ta Darekta Janar ta kungiyar NGF, an fahimci jihohi ba su ci bagas ba, an sanar da shugaban kungiyar gwamnoni na kasa hakan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Asishana Okauru ya ce idan gwamna bai sha’awar tallafin, ya na da damar janye hannunsa, iyaka ya dawo da Naira biliyan biyu da aka ba su.

"AbdulRahman AbdulRazaq ya umarce ni da in gabatar da bayanin kudin kamar haka:
Girman kudin: N4,000,000,000.00
Bashi (48%): N1,920,000,000.00
Tallafin Gwamnatin tarayya: 52%
N2,080,000,000.00 ga kowane Gwamnati
Masu amfana: Gwamnatocin jihohi
Lokacin biyan bashi: Watanni 20
Ruwan bashi: 0%
Karin lokacin biya: Watanni 3
Yanayin biyan bashi: A kowane wata
Kudin da za a biya: N120,000,000.00
ISPO"

- Asishana Okauru

Ana da labari Bola Tinubu ya ce shawo kan matsalolin sai an yi hakuri, ba sha yanzu magani yanzu ba ne, shugaban kasar ya bukaci a bi a hankali.

Amma duk da haka shugaban kasar ya na ganin mulkin Najeriya bai da wahala sosai. George Akume ya bayyana haka wajen kaddamar da littafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng