Mulki Babu Wahala, Amma Babu Wata Hanyar Gaggawa Wajen Gyara Kasa - Tinubu
- An buga littafi game da rayuwar dattijon Neja-Delta, Edwin Clark wanda aka kaddamar a makon nan
- Shugaba Bola Tinubu ya samu wakilci daga George Akume wajen kaddamar da littafin a birnin Abuja
- Mai girma shugaban Najeriya ya ce sai an hada da hakuri kafin a gyara matsalolin da ke addabar kasar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Magance matsalolin da su ka dabaibaye Najeriya ba tamkar kwankwadar shayi ba ne, Bola Ahmed Tinubu ya ce a sannu za a gyara kasar.
Tribune ta ce shugaban Najeriyan ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da littafin da aka rubutu a kan tarihin Edwin Clark.
A jawabin da ya yi ranar Alhamis a Abuja, Mai girma Bola Tinubu ya amsa cewa a maganar da ake yi, kasar nan ta shiga cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan
Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Raddi Kan Zargin Zaluntar ‘Yan Arewa a Rabon Mukaman Minista

Asali: Twitter
Ana kuka da wahalar rayuwa
Janye tallafin fetur da aka yi ya jawo al’umma su na kukan cewa rayuwa ta kara wahala.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A nan ne aka ji shugaban Najeriyan ya na bayanin cewa gwamnatinsa ta fara rabon kayan tallafi kamar abinci da samar da motocin jigilar mutane.
Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume wanda ya wakilci Bola Tinubu a wajen kaddamar da littafin ya ce Najeriya ta na da matukar sarkakiya.
Amma duk da haka, Sanata George Akume ya ce tafiyar da mulkin Najeriya ba ta da wahala.
Rahoton Vanguard ya kara da cewa gwamnatin Tinubu na daukar yawa da bambance-bambance ta fuskar addini da kabilanci a matsayin karfi.
"Tun da (Bola Tinubu) ya zo ya nuna ya iya kula da bambancin nan ta hanyar nada mutane ga muhimman mukamai.

Kara karanta wannan
Komai Ya Lafa, Majalisa Ta Fadi Inda Aka Samo Miliyoyin ‘Hutun’ da Aka Biya Sanatoci
Babu mutumin yankin kudu maso gabas da ya rike kujerar Ministan ayyuka. Wannan na cikin la’akari da bambancin."
- George Akume
Akume ya shaidawa wadanda su ka halarci taron cewa wahalar da ake sha a yau tamkar irin na mahafiya ne a lokacin nakuda, saboda ta haifi jariri.
Badaru, Mamman da Abubakar Kyari
Wani daga cikin Hadiman shugaban kasa Bola Tinubu, Abdulaziz Abdulaziz ya ce masu son rai ne zai su ce ba a kyautawa Arewa wajen zaben ministoci ba.
Matsalolin Arewa su ne tsaro, ilimi da aikin noma, Abdulaziz yake cewa duka ma’aikatun uku an damƙa su a hannun mutanen Arewa ne dai ba kowa ba.
Asali: Legit.ng