Majalisa Ta Fadi Inda Aka Samo Miliyoyin Kudin Hutun da Aka Biya Sanatoci 109
- Akawun majalisar tarayya ya fayyace gaskiya game da kudin da aka biya Sanatoci a makon jiya
- Miliyoyin da aka rabawa ‘yan siyasar ya jawo ana maganganu saboda yadda abin ya fito fili wannan karo
- Sani Tambuwal ya tabbatar da cewa doka ta san da kudin, an saba biya a duk lokacin tafiya hutu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Shugabannin majalisar dattawa sun ce Naira miliyan 2 da kowane Sanata ya samu a makon jiya, ya na cikin kudin gudanar da aiki.
Premium Times ta ce Akawun majalisar tarayya ya fitar da jawabi ta bakin Sakataren bincike da yada labarai na majalisa, Alhaji Ali Umoru.
Sani Tambuwal ya jawo karshen surutan da ake yi game da alawus da shugaban majalisa, Godswill Akpabio ya ce an biya kowane Sanata.
Kafin su tafi hutun wata biyu, an kashe fiye da Naira miliyan 200 a kan ‘yan majalisar. Ali Ndume ya na ganin hakan ba komai ba ne.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Alawus din da ake magana ya na cikin kundin kasafin kudin 2023 a matsayin kudin gudanar da aikin kowane Sanata a majalisa ta 10.
Saboda haka alawus din hakkokinsu ne ba alfarma ko makudan kudi ne da aka rabawa Sanatocin ba.
Amma ganin yadda aka yi wa abin wani mummanan kallo, ya zama dole a fito ayi wannan bayani domin yin karin haske, a fayyace komai.
Majalisar tarayya da gaske ta ke yi na tabbatar da gaskiya wajen kula da dukiyar al’umma.”
- Sani Tambuwal
Sanatoci sun ci halal
Tribune ta rahoto Sani Tambuwal ya na cewa abin da aka biya bai saba ka’ida ba, ya na cikin al’adar da tayi shekara da shekaru a majalisa.
Abin da doka ta ce shi ne Sanata ya na karbar 10% na albashin shekara a duk lokacin da ya tashi tafiya hutun da su ke zuwa lokaci zuwa lokaci.
Idan har an yi kasafin alawus din kuma RMAFC ta san da zaman su, ba za a ce an saba doka ba, akasin abin da rahotanni su ka nuna a baya.
Majalisa ta na son karin Ministoci
Ku na da labari Ministoci biyar kacal za a nada daga Kudu maso gabas, amma an warewa sauran yankuna kujerun da ya zarce adadin na su.
Duka sanatocin jihohin yankin Ibo da ke majalisar dattawa sun ce adalcin da Bola Tinubu zai yi shi ne ya kara masu Ministoci ko da biyu ne.
Asali: Legit.ng