Matan Aure Sunyi Zanga-Zanga Kan Yunwa Da Tsadar Abinci A Kaduna

Matan Aure Sunyi Zanga-Zanga Kan Yunwa Da Tsadar Abinci A Kaduna

  • Wasu matan aure a karamar hukumar Igabi sun yi zanga-zangar lumana don nuna damuwa kan halin da ake ciki
  • Matan su ka ce sun fito ne don rokon Shugaba Tinubu ya yi wani abu don kawo karshen tsadar abinci da yunwa
  • Wata dattijuwa mai shekaru 60 ta tabbatar da cewa akwai yara biyu da su ka mutu saboda tsabar yunwa a garin

Jihar Kaduna – Matan aure daga garin Rigasa da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna sun gudanar da zanga-zangar lumana don nuna damuwarsu da halin da ake ciki.

Matan auren da suka hada da yaransu sun yi wannan tattaki ne musamman don nuna damuwa da irin yunwa da ake ciki da tsadar kayayyaki.

Matan aure sun yi zanga-zanga a Kaduna kan tsadar abinci da yunwa
An Gudanar Da Zanga-Zangar Ne Don Nuna Damuwa Da Halin Da Ake Ciki. Hoto: Leadership.
Asali: Facebook

Meye dalilin yin zanga-zangar a Kaduna?

Matan sun mamaye titunan garin tare da ihun cewa “Tinubu mu na jin yunwa", Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Sheikh Ahmad Gumi Ya Tona Masu Karkatar da Shugaba Tinubu da Muguwar Shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikinsu sun roki Shugaba Bola Tinubu da ya kawo musu dauki inda su ka ce ba su taba shiga irin wannan hali ba.

Wata dattijuwa duk da rashin lafiyarta ta samu shiga cikin masu zanga-zangar da ‘ya’yanta marayu guda biyar da ta ce su na matukar bukatar abinci mai gina jiki.

Meye ma su zanga-zangar a Kaduna ke bukata?

Ta bayyana cewa rasuwar kanin mijinta wanda ya dadeya na taimaka musu bayan rasuwar mijinta shi ya jefata cikin wannan hali inda ta ce babu yadda ta iya dole rokon jama’a ta ke don samun abin tabawa.

Wata dattijuwa mai shekaru 60 ta bayyana cewa yara biyu a garin sun mutu saboda tsananin yunwa inda ta alkanta hakan da rashin iya kawo abinci daga iyayensu, cewar Leadership.

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa ba wai taimakonsu su ke son a yi ba, amma su na rokon Shugaba Tinubu da ya kawo karshen tsadar abinci saboda su sa mu su siya a farashi mai rahusa.

Kara karanta wannan

Cin Hanci: Abba Gida Gida Ya Tsorata, Ya Bukaci Binciken Gaggawa A Kotun Sauraran Korafe-Korafen Zabe

Matan Kaduna Sun Yi Zanga-Zanga Kan Zaben Gwamna

A wani labarin, dandazon mata daga jihar Kaduna musamman na jam'iyyar PDP sun fito zanga-zanga don nuna adawa da zaban Uba Sani a matsayin Gwamna.

Matan sun cika birnin Kaduna sanye da bakaken kaya inda su ke fadin cewa ba su yadda da wannan zabe ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.