Abba Gida Gida Ya Bukaci Yin Bincike A Badakalar Cin Hanci A Kotun Kararrakin Zabe

Abba Gida Gida Ya Bukaci Yin Bincike A Badakalar Cin Hanci A Kotun Kararrakin Zabe

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya nuna damuwarsa kan badakalar cin hanci a kotun kararrakin zabe
  • Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin kwamishinan yada labarai a jihar, Baba Halliru-Dantiye inda ya bukaci daukar matakin gaggawa
  • Ya ce dole hukumar yaki da cin hanci su yi abin da ya kamata don binciko tare da hukunta masu hannu a ciki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya nuna damuwarsa kan zargin ba da cin hanci ga alkalai a shari'ar zabe da ake a jihar.

Shugabar kotun sauraran kararrakin zabe na majalisun Tarayya da na jiha, Flora Ngozi Azinge ita ta bayyana wannan badakalar da ke faruwa inda ta ce manyan lauyoyi sun tsunduma ciki.

Abba Kabir ya bukaci bincike kan cin hanci ga alkalai a Kano
Abba Gida Gida Ya Bukaci Yin Bincike Kan Cin Hanci Ga Alkalai. Hoto: The Guardian.
Asali: Facebook

Me Abba Gida Gida ke zargi?

Kara karanta wannan

El-Rufai: APC Ta Bukaci Tinubu Ya Maye Gurbin Minista Daga Kudancin Kaduna, Ta Fadi Wanda Ya Kamata

Idan ba a manta ba Azinge ta fada cewa akwai wasu da ke son ba wa mamban kwamitinsu cin hanci don sauya akalar shari'ar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta koka yadda manyan lauyoyi su ka tsunduma cikin badakalar kafin zaman kotu a ranar Talata da ta gabata a Kano, Daily Nigerian ta tattaro.

Yayin da ya ke martani a yau Alhamis 17 ga watan Agusta, kwamishinan yada labarai a jihar, Baba Halliru-Dantiye ya nuna damuwarsa kan lamarin.

Dantiye ya bayyana damuwarsa da cewa wasu marasa daraja na kokarin kawo cikas ga dimokradiyya a jihar.

Ya ce:

"Mun samu labarin badakalar cin hanci a shari'ar da ake kan zabe wanda Ngozi Azinge ke jagoranta ta tabbatar."
"Azinge ta tabbatar da ana ta wasa da kudade a shari'ar da nufin ba da cin hanci don karkatar da akalar shari'ar.

Kara karanta wannan

Shari'ar Gwamnan Kano: Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Roki Yan Najeriya Su Taya APC Addu'ar Samun Nasara Kan PDP

Wane mataki Abba Gida Gida zai dauka?

Ya ce wannan kalubale ne ga gwamnatin jihar da ke kokarin yaki da cin hanci inda ya ce za su bincike lamarin da kuma hukunta masu hannu a ciki.

Ya kara da cewa:

"Ya kamata hukumomin yaki da cin hanci su dauki mataki a kan wannan mummunan al'amari da babbar lauya ta tabbatar."

Kwamishinan ya godewa Azinge inda ya ce har yanzu akwai mutanen kwarai musamman a harkar shari'ar kasar, cewar Leadership.

Ya godewa mutane jihar da irin kokarin su na zaban NNPP da kuri'u fiye da miliyan daya ba tare da gwamnati a hannunsu ba, inda ya musu alkawarin dakile masu son kawar da gwamnatin.

Abba Kabir Ya Rantsar Da Mace Ta Farko Alkaliyar Alkalai

A wani labarin, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya rantsar da mace ta farko Dije Audu Aboki a matsayin alkaliyar alkalan jihar.

Kara karanta wannan

Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati

Wannan shi ne karon farko da aka taba tabbatar da mace a jihar a matsayin shugabar alkalai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.