‘Yan Ta’adda Sun Shirya Sake Kai Wani Hari a Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Inji SSS
- Wani binciken jami’an tsaro na DSS ya gano ana neman a kai hari a jirgin kasa na Abuja-Kaduna
- Shekara da rabi bayan abin da ya faru da fasinjoji a jejin Kaduna ‘Yan bindiga ba su hakura ba
- Hukumar DSS ta sanar da NRC cewa ana so ayi garkuwa da fasinjoji domin a karbi kudin fansa
Abuja - Maganar da ake yi shi ne ana zargin ‘yan ta’adda su na tsara yadda za su yi domin su kai hari a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a Najeriya.
Rahoton Premium Times ya ce burin wadannan ‘yan ta’adda shi ne su yi garkuwa da fasinjoji. Hukumar DSS ta ankarar da NRC halin da ake ciki.
Jami’an tsaro masu fararen kaya, sun aika takardar tsaro ta sirri zuwa shugaban NRC mai kula da jiragen kasa domin sanar da shi abin da ke faruwa.
Za a iya kai hari a ko yaushe
A wannan wasika ta ranar 11 ga watan Agusta da wasu su ka bankado kuma aka fitar da ita a fili, an fahimci a ko yaushe miyagun za su iya kai harin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Gungun miyagun ‘yan bindiga su na shirya kai hari a jirgin kasan kowane lokaci daga yanzu."
- Wasikar DSS
Ba yau 'Yan bindiga su ka fara ba
Idan za a tuna, a shekarar 2022 an kai wani mumunnan hari wajen jejin Kateri-Rijana, aka yi awon gaba da fasinjoji masu dawowa daga birnin Abuja.
An rasa rayuwan Bayin Allah akalla takwas a sakamakon harin ‘yan ta’addan bayan garkuwa da fasinjoji kimanin 100 da aka yi daga jirgin a cikin dare.
Shakka babu hakan babbar barazana ce ta fuskar tsaro da tattalin arziki, abin da ya fi ban tsoro shi ne yadda takardun sirri su ke fitowa shafin yanar gizo.
Saboda haka ne jaridar ta ce SSS a wancan lokaci ta ba NRC shawarwarin yadda za a gujewa sake aukuwar irin wannan lamari da ye jefa kasar a dar-dar.
Wani hali ake ciki a NRC?
Babu tabbacin ko an yi amfani da shawarar da jami’an tsaron su ka bada bayan an dawo aiki.
Da aka tuntubi manajan jirgin a tashar Abuja, Pascal Nnorli, a makon nan ya shaidawa manema labarai bai tattauna sha’anin tsaro ta wayar salula.
Duk wanda bai ji bari ba...
Ana da labari Gwamnan Kaduna a lokacin, Malam Nasir El-Rufai ya ce sun fadawa hukumar jirgin a daina daukar fasinjoji da dare, amma ba a saurare su ba.
Rotimi Amaechi a lokacin ya na ministan sufuri, ya nuna cewa akwai kayan aikin da ya kamata gwamnatin tarayya ta tanada a hanyar jirgin, amma ba ayi ba.
Asali: Legit.ng