Da dumi dumi: Yan bindiga sun kai ma jirgin Kaduna – Abuja hari

Da dumi dumi: Yan bindiga sun kai ma jirgin Kaduna – Abuja hari

Wasu gungun yan bindiga sun bude ma jirgin kasa wuta a kan hanyarsa ta zuwa babban birnin tarayya Abuja daga jahar Kaduna, inji rahoton jaridar Vanguard.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jirgin ya tashi daga tashar jirgin kasa dake garin Rigasa na jahar Kaduna da misalin karfe 10 na safe, sai dai bai yi nisa ba ya ci karo da yan bindiga a daidai garin Katari, kimanin kilomita 70 kafin shiga Abuja.

KU KARANTA: An yi biyu babu: Magidanci ya daddatsa uwar matarsa, sa’annan ya halaka kansa

Wani fasinja dake cikin jirgin ya tabbatar ma majiyarmu cewa yan bindigan sun yi amfani da ababen harbe harbe da dama wajen kai ma jirgin hari, amma dai babu fasinjar daya jikkata a dalilin harin.

Ku biyo mu domin samun cigaban labarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng