Shehu Sani Ya Yi Martani Yayin da Tinubu Ya Nada Matawalle Ministan Tsaro
- Tsohon dan majalisa, Sanata Shehu Sani, ya yi martani kan yanayin aikin da Tinubu ya rabawa ministocinsa
- Sani ya kalubalanci shugaban kasa Tinubu da bai nada tsohon soja da ke da kwarewa da sanin aiki a matsayin ministan tsaro ba
- Tinubu ya rabawa ministocinsa gaba daya ayyukan da za su kama a ranar Laraba, 16 ga watan Agusta
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kaduna - Tsohon sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya nuna damuwarsa matuka yayin da shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Muhammad Badaru, tsohon gwamnan jihar Jigawa a matsayin ministan tsaro.
Haka kuma, Tinubu ya nada tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle a matsayin karamin ministan tsaro a ranar Laraba, 16 ga wata Agusta.
Sani a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a daren Laraba, ya yi mamaki kan dalilin da yasa ba a nada tsohon soja a matsayin ministan tsaro ba yayin da Najeriya ke fuskantar matsalolin tsaro a yanzu haka.
Da yake martani ga ayyukan da aka rabawa ministocin shugaban kasa Tinubu, mako guda bayan majalisar dattawa ta tantance su, Sani ya rubuta:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"A nawa ra'ayin da matsalolin tsaro da kasar nan ke fuskanta, na yi zaton ya kamata ministan tsaro ya zama tsohon soja da ke da kwarewa da tarihin nasarorin da ya samu. Bai kamata wannan ofishin ya zama na siyasa kawai ba, musamman a wannan lokaci."
Jama'a sun yi martani
@legend_082 ya rubuta:
"Ministan sufurin jiragen sama lauya ne wanda bai da masaniya ko kadan a kan ma'aikatar."
@CyrusAdemola ya yi martani:
"Me za mu iya cewa? ministan tattalin arziki da kasafin kudi, Atiku Bagudu, yana da zarge-zargen rashawa a wuyansa tun daga zamanin Abacha. Sanata duk neman suna ne."
@TimiBlaze ya ce:
"Na zata baka damu da rashawa ba? "
@BelloMuhammad12 ya rubuta:
"Wata irin kasa Bello Matawalle a matsayin karamin ministan tsaro a lokacin gwamnatinsa a matsayin gwamna ya rabawa shugabannin yan bindiga motocin Toyota Hilux a matsayin kyauta."
NNPC ya karbo bashi don farfado da naira
A wani labarin, mun ji cewa, Kamfanin mai na NNPC ya ciwo bashin Dala biliyan uku don kawo daidaito a darajar Naira.
Kamfanin ya samu nasarar ciwo bashin ne a bankin AFRIEXIM da ke birnin Cairo a kasar Masar.
Asali: Legit.ng