Daga Karshe Lauya Ya Gano Ainahin Masu Gidan Da Aka Yasar Tsawon Shekaru 30 a Kaduna, Hotuna Sun Bayyana

Daga Karshe Lauya Ya Gano Ainahin Masu Gidan Da Aka Yasar Tsawon Shekaru 30 a Kaduna, Hotuna Sun Bayyana

  • An gano aimahin mai wani gida a jihar Kaduna da aka yasar da shi tsawon shekaru 30 da suka gabata
  • Wani lauyan Najeriya ya dauki nauyin yin bincike sannan ya bazama neman ainahin mai gidan bayan ya ga yadda mutane daban-daban suka yi amfani da damar wajen mallakar sa
  • Ya yada hotunan ainahin mai gidan a gidan sannan ya bayar da karin haske kan wanda zai dunga kula da gidan har zuwa gaba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kaduna - Wani lauyan Najeriya, Abdulmalik A Othman, ya sha jinjina a soshiyal midiya bayan ya jagoranci nemo ainahin mammalakan wani gida da aka yasar tsawon shekaru 30 a jihar Kaduna.

Lamarin ya fara ne bayan lauyan, wanda ke gudanar da kamfanin lauyoyi 'Limelight Attorneys', ya lura da gidan da aka yi watsi da shi a makwabtansa sannan ya daurawa kansa alhakin nemo ainahin masu shi.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Dan Adaidaita Ya Jera Tankunan Ruwa 13 a Kan Keke Ya Girgiza Intanet

Abdulmalik ya bazama neman masu gidan a soshiyal midiya
Daga Karshe Lauya Ya Gano Ainahin Masu Gidan Da Aka Yasar Tsawon Shekaru 30 a Kaduna, Hotuna Sun Bayyana Hoto: Abdulmalik A Othman
Asali: Facebook

Don cimma hakan, sai ya kaddamar da wani gangami a dandalin soshiyal midiya kamar su Facebook da Twitter da wasu tsoffin hotunan ainahin masu gidan.

Wannan kokari nasa ya cimma nasara domin ya hadu da iyalin kuma sun ziyarci gidansu da aka yi watsi da shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wani wallafa da ya yi a Facebook, Abdulmalik ya bayyana cewa iyalin sun fara barin gidan a 1994 saboda rikicin addini. Sai su dawo daga baya sannan suka sake ficewa a 2005 saboda dalili iri guda.

Ya ci gaba da bayani:

"Bayan sun fice, sun mika gidan a hannun wani da suka aminta da shi wanda yake abokin iyalin ne kuma tun daga lokacin ba su sake waiwayansa ba saboda yawanci suna wajen jihar/kasar. Wannan aminin iyalin bayan ya zauna na tsawon shekaru sai ya kawo wani sannan ya tafi ba tare da ya sanar da su ba sannan wannan ma ya kawo wani sannan aka ci gaba da haka har zuwa kan mutanen da ke cikin gidan a yanzu."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Rundunar Sojoji Ta Bayyana Adadin Dakarunta Da Yan Ta’adda Suka Kashe a Neja

A yanzu an mika gidan mai dakunan kwana hudu da bangaren maza a hannun kamfaninsa don kula da shi. Da yake tabbatar da haka, Abdulmalik ya rubuta:

"...A karshe, an yafe dukkan batutuwan kuma an manta sannan an ci gaba da rayuwa, an nada kamfanina 'Limelight Attorneys LLP' domin kula da gidan gaba daya kuma duk lamuran da ya shafe shi."

Da Legit.ng ta tambayi Abdulmalik game da nadin nasa, matashin ya ce bai taba hango zuwan hakan ba. Ya saki hotuna daga ziyarar baya-bayan nan da masu gidan suka kawo.

Jama'a sun yi martani

Garba Musa Ahmad ya ce:

"Doka! Allah ya haskaka zuciyarka bugu da kari za a iya magance irin wadannan shari'o'i bisa doka da hikima."

Chioma Umezinwa Onuoha ta ce:

"Na gode yallabai, ka yi gagarumin aiki..Na yi imanin irin wadannan shari'o'in za su shafi Jos, saboda rikicin cikinsa ma...an gode da Allah ya bar rai..."

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Karin Bayani a Kan Yiwuwar Dawo da Tallafin Man Fetur

Idris Muhammad Ngene ya ce:

"Lamura irin haka na faruwa sosai. A Abuja misali, za ka ga mutane na zaune a gidan kyauta saboda mamallakinsa ya mnutu kuma yan uwa basu san da gidan ba sannan su ci gaba da mika shi daga wannan zuwa wannan. Na san wani da ya zauna a gidan kyauta na tsawon shekaru kuma da ta tadu. Ta mikawa wani saboda mai gidan bai zo ba da dadewa."

Malamar makaranta ta yi wa dalibarta zane

A wani labari na daban, mun ji cewa wata uwa ta ce wata malamar makaranta ta sharbawa diyarta zane guda hudu a fuska ba tare da izini ba.

Wani hoton yarinyar da shafin gidan radiyon Ilorin, Sobi Fm, ya wallafa a Facebook ya nuno yarinyar dauke da zane hudu a gefen kuncinta na dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng