Yan Bindiga Sun Harbe Matar Wani Malamin Addini Har Lahira a Jihar Edo

Yan Bindiga Sun Harbe Matar Wani Malamin Addini Har Lahira a Jihar Edo

  • Tsagerun yan bindiga sun farmaki wani fasto, Rev. Samuel Chinyereugo da matarsa a garin Benin, jihar Edo
  • Maharan sun sha gaban motar malamin addinin sannan suka bude masu wuta, lamarin da ya yi sanadiyar rasa ran matarsa, Misis Peace Chinyereugo
  • Rundunar yan sandan jihar Edo ta tabbatar da lamarin, inda ta ce ta kaddamar da bincike a kan lamarin

Jihar Edo - Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun harbe Misis Peace Chinyereugo, matar faston cocin Vineyard of Grace Dominion Assembly, Rev. Samuel Chinyereugo, a garin Benin, babban birnin jihar Edo.

Lamarin ya afku ne da misalin karfe 7:36 na yammacin ranar Litinin, 14 ga watan Agusta, a harabar cocin da ke lamba ta 101, Unguwar Upper Lawani, New Benin, garin Benin, rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Yi Layar Zana Da Motar Miliyan 23 Da Aka Ba Shi Wanki, An Saki Hotonsa a Soshiyal Midiya

Yan bindiga sun halaka matar fasto
Yan Bindiga Sun Harbe Matar Wani Malamin Addini Har Lahira a Jihar Edo Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Yadda yan bindiga suka kashe matar fasto a jihar Edo

An tattaro cewa malamin addinin da matarsa sun kai ziyara gidan wani abokinsa a GRA, inda yan bindigar suka dungi bin su har zuwa cocin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai da suka kusa da cocin, an tattaro cewa sai maharan suka sha gabansu sannan suka toshe motarsu.

Wasu shaidu sun bayyana cewa yan bindigar guda uku sun fito daga motarsu sannan suka budewa faston, matarsa da wani hadiminsa da ba a ambaci sunansa ba wuta.

An nakalto faston ya bayyana cewa ya lura da wata mota tana binsa a cikin GRA, inda ya ziyarci abokinsa don haka ya kadu da ya ga wannan motar ta sha gabansa a gaban cocinsa, rahoton Newtelegraph.

An kwashi su dukka ukun zuwa wani asibiti, inda daga bisani likitan ya tabbatar da mutuwar matar faston.

Kara karanta wannan

Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati

Rundunar yan sanda ta kaddamar da bincike

Kakakin rundunar yan sandan jihar Edo, SP Chidi Nwabuzor, wanda ya tabbatar da kisan ya ce ba a kama kowa ba kan lamarin zuwa yanzu.

Sai dai kuma, ya bayyana cewa rundunar ta fara gudanar da cikakken bincike don gano wadanda suka aikata ta'asar da kuma hukunta su.

Yan bindiga sun sace malamin Musulunci da matarsa a Kaduna

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu da ake zaton yan bindiga ne sun yi garkuwa da wani malamin addinin Musulunci, Malam Abubakar Mushawy Ibrahim, tare da matarsa da yaransu biyu a jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa daya dana cikin yaran ya kasance jariri dan kwana daya lokacin da aka yi garkuwa da su a ranar Laraba da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng