"Ka Yi Murabus Idan Ba Za Ka Iya Ba”, Hadimin Matawalle Ga Dauda Lawal Na Zamfara
- Hadimin tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, Kwamred Abdullahi Kaura ya soki Gwamna Dauda Lawal kan tabarbarewar tsaro
- Kaura ya bayyana haka ne a yau Laraba 16 ga watan Agusta inda ya bukaci gwamnan da ya yi murabus idan ba zai iya ba
- Ya ce kai hare-hare da sace mutane ya yi kamari a jihar tun bayan hawan Gwamna Dauda Lawal karagar mulki
Jihar Zamfara - Ganin yadda rashin tsaro ke kara ta'azzara a jihar Zamfara, an kirayi Gwamna Dauda Lawal Dare da ya yi murabus.
Kwamred Abdullahi Anas Kaura, hadimin tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle shi ya bayyana haka a yau Laraba 16 ga watan Agusta.
Legit.ng ta tattaro cewa Kaura ya zayyano tarin matsalolin da su ka shafi jihar tun bayan hawan Dauda Lawal mulki.
Me ake zargin gwamna Zamfara da shi?
Ya zargi gwamnan da ba wa baki damar rike akalar jihar wanda hakan ke kawo cikas a kokarin dakile matsalar tsaro.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cikin sanarwar, ya bukaci gwamnan da ya dauki tsauraran matakai don kawo karshen rashin tsaro da kuma matsanancin talauci da ta addabe su.
Ya ce:
"Akwai wasu tsare-tsare na tsohuwar gwamnatin da ta shude, idan gwamna mai ci ya yi amfani da su zai iya cin nasara a harkar tsaro da rage talauci."
Me aka bukaci gwamnan Zamfara ya yi?
Ya koka kan yadda gwamnan ya gaza wurin biyan albashin ma'aikata inda ya bukaci ya yi murabus idan abin ya fi karfinsa.
Kaura ya yi Allah wadai da yadda garkuwa da mutane da kuma kashe-kashe ya karu a dan lokacin da Gwamna Dauda ya hau mulki.
Babban Hafsan Sojojin Najeriya Ya Fadi Irin Matakan Da Za Su Dauka a Kan 'Yan Ta'addan Jihar Zamfara
Ya kirayi 'yan jihar da su ci gaba da hakuri musamman magoya bayan jam'iyyar APC, cewar Vanguard.
Sojin Sama Sun Yi Ajalin Aliero Da Dankarami A Zamfara
A wani labarin, rundunar sojin sama a Najeriya ta yi luguden wuta kan wasu 'yan ta'adda inda su ka yi nasarar hallaka manyan shugabannin 'yan bindiga Ado Aliero da Dankarami.
Rundunar ta kai samamen ne bayan samun bayanan sirri a kananan hukumomin Zurmi da Tsafe a jihar Zamfara inda su ka yi nasarar tarwatsa maboyar 'yan bindiga.
Asali: Legit.ng