Sunusi Lamido Ya Ce 'Yan Najeriya Ne Su Ka Ba Da Dama Ga 'Yan Siyasa Ke Wulakanta Su

Sunusi Lamido Ya Ce 'Yan Najeriya Ne Su Ka Ba Da Dama Ga 'Yan Siyasa Ke Wulakanta Su

  • Tsohon sarkin Kano, Sunusi Lamido ya ce idan har wadanda ba su shiga siyasa ba, na tsoron fadan gaskiya to za a samu matsala a kasar
  • Ya ce idan ba a binciken ‘yan siyasa a kan kura-kurensu to za su kashe kasar yadda wadanda za su zo daga baya za su gagara nuna kasarsu
  • Sunusi ya fadi haka ne a cikin wani bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta inda ya ce da ya shiga siyasa da watakila ya zama gwamna

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano – Tsohon sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi ya bayyana cewa ‘yan Najeriya su ka ba wa ‘yan siyasa damar ci musu mutunci.

Sunusi ya ce idan ba a binciken ‘yan siyasa a kan abinda su ke aikatawa to masu zuwa nan gaba ba za su iya kiran Najeriya kasar su ba.

Kara karanta wannan

Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati

Sunusi ya yi gargadi kan yadda 'yan Najeriya su ka rena kansu
Sunusi Ya Koka Kan Yadda ’Yan Najeriya Su Ka Ba Wa 'Yan Siyasa Damar Rena Su. Hoto: The Guardian.
Asali: Facebook

Ya ce don mafi yawan ‘yan Najeriya ba su shiga siyasa ba, hakan ba wai ya na nuna su makaskanta ba ne, cewar Vanguard.

Sunusi na magana ne a cikin wani faifan bidiyo da ake yadawa a kafafen sadarwa inda ya ce babu wani mahaluki da zai ci zarafin ‘yan Najeriya su bar shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

“Babu wanda zai mana barazana saboda shi shugaban kasa ne ko gwamna, dole mu fadi gaskiya idan sun yi ba daidai ba.
“Mun dauki wata hanya daban a rayuwa, idan da ace harkar siyasa na shiga, ganin yadda mutane ke da alaka da shugaban kasa, da zan iya zama shugaban kasa ko gwamna.
“Don ban zabi shiga siyasa ba, hakan ba ya na nufin ni kaskantacce ba ne, wannan shi ne abin da ya kamata mu koya a matsayin mu na ‘yan Najeriya.”

Kara karanta wannan

Muddin Aka Sake Kara Farashin Fetur, Za Mu Birkita Kasar Nan da Yajin Aiki Inji NLC

Sunusi ya kara da cewa ‘yan Najeriya su ka ba wa ‘yan siyasa dama har su ke cin kashi a kansu, idan muka bari hakan ya ci gaba to lallai ‘yan baya ba za su kira Najeriya kasar su ba.

Ya kara da cewa:

“ Mu muke ba su dama su ke cin kashi a kan mu, duk lokacin da ‘yan siyasa su ka gama da mu, ‘ya’yanmu da za su zo daga baya za su rasa inda za su kira kasarsu.
“Hanya daya ce na gyara kasar da kuma samar wa ‘ya’yanmu rayuwa a gaba, shi ne idan ba ka shiga siyasa ba, ka fadawa ‘yan siyasa gaskiya idan suka yi kuskure.”

Tinubu Na Ganawa Na Musamman Da Sunusi Lamido

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya na wata ganawa da tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi a fadarsa.

Wannan shi ne karon farko da tsohon sarkin ke ganawa da Bola Tinubu tun bayan hawan shi mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.